Martanin ƙungiyoyi ga zaɓen Nijar | Labarai | DW | 01.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin ƙungiyoyi ga zaɓen Nijar

Ƙungiyoyin farar hula 32 da suka sanya ido akan zaɓen raba gardama a Nijar sun lissafta kura kurai 19 da suka ce an tafka a lokacin sa

default

Shugaba Salou Djibo tare da wakilin MƊD Said Djinnit, da kuma Ramtane Lamamra na AU

Ƙawancen ƙungiyoyin farar hular na cikin gida a jamhuriyyar Nijar waɗanda yawan su yakai 32n da suka yi aikin sanya ido akan zaɓen raba gardama akan sabon tsarin mulkin ƙasar - a jiya Lahadin, sun bayyana cewar akwai kura kuran da aka tafka a lokacin zaɓen. Ƙawancen ƙungiyoyin sun sanar da hakan ne a lokacin wani taron manema labaran da suka kira a Niamey, fadar gwamnatin Nijar, inda suka bayyana rahoton su dangane da yadda zaɓen ya gudana.

Malam Sule Umaru ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyoyin farar hular daya dubi yadda zaɓen ya wakana ya ce baya ga rashin fitowar jama'a kamar yadda ya kamata, akwai kuma wasu kura kuran da suka haɗa da rashin samun sunayen masu zaɓe a kundin rajista da kuma rashin bayar da horon daya kamata ga jami'an aikin zaɓen.

Sai dai kuma duk da irin kura kuran da ƙungiyoyin suka bayyana, amma sun yabawa hukumar zaɓen Nijar da kuma jami'an tsaron ƙasar wajen ɗaukar matakan ganin cewar aikin ya gudana cikin nasara.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Mohammad Nasiru Awal