Martanin ƙasashen tekun fasha ga nukiliyar Iran | Labarai | DW | 23.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin ƙasashen tekun fasha ga nukiliyar Iran

ƙasar haɗaɗɗiyar daular larabawa ta baiyana cewa ƙasashen larabawa na yankin tekun fasha na shirin tattaunawa da Iran a game da damuwar su kan haɗarin da shirin nukiliyar Iran ɗin zai haifar ga yanayin muhalli na ƙasashen dake makwabtaka da ita. Ministan harkokin waje ƙasar Sheikh Abdullah bin Zayed al-Nahayan ya gabatar da batun gurbatar muhallin a taron manema labarai da ya gudanar tare da ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier wanda ya kai ziyarar rangadi a ƙasar. Sheikh Abdullah bin Zayed yace sabanin ƙasar Iran, sauran ƙasashen larabawa dake yankin tekun fasha sun dogara ne ga ruwan teku wajen samun ruwan sha da kuma ban ruwa na kayan lambu. Yace idan ruwan ya gurbace a sakamakon harkokin nukiliyar, zai shafi yanayin rayuwar alúmomin yankin baki ɗaya. Ministan yace nan ba da jimawa ba wata tawaga mai karfi wadda za ta kunshi kwararun masana muhalli dana tattalin arziki daga ƙasashen Saudiya da Kuwait da Bahrain da Oman da Qatar da kuma hadaddiyar daular larabawa za su kai ziyara birnin Tehran domin ganawa da mahukuntan Iran a game da batun. Abdullah bin Zayed yace yana fata ƙasar Iran din ta Islama zata nuna hakuri da fahimta a game da bukatun na su.