1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin ƙungiyoyin Duniya kan rikicin Jos

March 9, 2010

Rigingimun da suka ritsa da jihar Filato na cigaba da samun suka daga ƙasashen Duniya

https://p.dw.com/p/MOIM
Hoto: AP

Ƙasashen Duniya, ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama da masu zaman kansu na cigaba da yin Allah wadan sabon rikicin daya ɓarke a jihar Filato tare da kira ga hukumomi dasu tashi tsaye wajen binciken sanadiyyarsa domin hukunta waɗanda keda alhaki.

Gwamnatin Amurka da ƙungiyar  kare haƙƙin jama'a ta ƙasa da ƙasa ta Human Rights watch sun yi kira ga Gwamnatin Nigeria da hukumomin da alhaki ya rataya a wuyansu a ƙasar, da su ɗauki matakan da suka dace na ganin cewar, an gurfanar da waɗanda ke da alhakin ɗorewan rikicin jihar Filato dayaki ci yaki cinyewa cikin 'yan shekaru da suka gabata.

Nigeria Massaka März 2010
Mata a rikicin Dogo NahawaHoto: AP

A cewar Ƙungiyar Human Rights watch ya zamanto wajibi mataimakin shugaban Nigeria Gooodluck Jonathan ya ɗauki matakan samar da sojoji da jami'an 'yan sanda da za su cigaba da samarwa al'ummar jos da kewaye kariya da tsaro.

Corinne Dufka dai itace mai bincike kan yammacin Afrika a ƙungiyar ta Human rights watch...

" munyi imanin cewar rashin hukunta waɗanda keda alhakin haifar da rigigimu na baya shike haifar da cigaban waɗannan rigingimu, domin masu aikata laifin walau musulmi, kristoci ko kuma jami'an tsaro kan ci karen su babu babbaka na kisan gilla, idan kuwa har ba'a gano waɗanda keda alhakin an hukunta su ba, za a cigaba da fuskantar wannan matsala"

Ita ma dai ƙungiyar ƙasashen musulmi ta OIC tayi Allah wadan wannan rikici  da ya jagoranci asarar ɗaruruwan rayukan mazauna ƙauyukan da aka kai hare-haren na jihar Filato.

Akan haka ne shugabanta Ekmeledin Ihsanoglu yayi kira ga mahukunta a tarayyar Nigeriya dasu ɗauki matakai na gano yadda za a kawo karshen wannan matsala na rigingimu tsakanin  manyan addinan ƙasar guda biyu.

A sanarwar daya gabatar, Ihsanoglu yayi kira ga al'ummomin Nigeriaya dasu koma teburin sulhujunta juna  domin inganta tubalin haɗin kai da zaman lafiya.

Kommissarin der Vereinten Nationen für Menschenrechte Navi Pillay
Navi PillayHoto: AP

Tuni dai gwamnatin Nigeriyar a ta bakin mataimakin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, tayi alkawarin binciken ummul aba'isin rigingimun na jihar Filato da ya ƙi ci ya ƙi cinye. Duk kuwa da cewar waɗannan alkawura ne da gwamnatin tasha ikirarin yi a baya ƙungiyar kare hakkin jama' a ta Human Right watch tayi maraba da wannan mataki kamar yadda Corrinne Dufka ta aiyana..

"" Muna marhabin da kalaman Jonathan na cewar bazai ɓata lokaci wajen tabbatar da cewar an gudanar da bincike tare da gurfanar da masu laifin gaban hukuma ba, ba tare da la'akari da kabila, addini kokuma kasancewarsu jami'an tsaro ba".

Ita ma dai hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Ɗunkin Duniya ta bayyan takaicinta dangane da wannan hali da Nigeriyar ta tsinci kan a ciki, tare ta kira ga mahukunta dasu shawo kan matsalolin talauci da wariya dake zama ummul aba'isin waɗannan rigingimu na kabilanci.

Shugabar hukumar Navi Pillay ta kwatanta rikicin ƙarshen makon daya bar kristoci da dama mace, da  kashe-kashen al'ummar fulani da akayi a watan janairu. Ta ce  waɗannan yanayi biyu  dai, mata da yara kanana sune abun kan ritsa dasu kai tsaye.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Ahmad Tijani Lawal