Martani kan zaɓen majalisar dokokin Jamus | Siyasa | DW | 27.09.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan zaɓen majalisar dokokin Jamus

Bayan shekaru huɗu na mulkin haɗin guiwa tsakanin Social Democrats da Christian Union, a yanzu an yi awon gaba da jam'iyyar SPD kuma nan gaba jam'iyyun Christian Union da Free Democrats ne zasu tafiyar da mulki a Berlin

default

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shuagabannin jam'iyyun da suka shiga zaɓen na shugaban gwamnati da majalisar dokokin da Bundestag sun mayar da martani a game da sakamakon zaɓen.

A haƙiƙa dai godiya ta tabbata ga gagarumar nasarar da jam'iyyar Free Democrats ta samu inda kawo yanzu alƙaluman da aka bayar suka ba ta kashi 15% na jumullar ƙuri'un da aka kaɗa, Angela Merkel zata samu kafar yin ta zarce duk kuwa da cewar jam'iyyun Christian Union sun sake samun koma baya a zaɓen. Ita kuwa jam'iyyar Social Democrats dake ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin waje Frank-Walter Steinmeier ta kwashi kashinta ne a hannu, saboda sakamakon wannan zaɓen shi ne mafi muni da ta taɓa fuskanta tun abin da ya kama daga shekara ta 1949. An saurara daga bakin Frank-Walter Steinmeier yana mai faɗin cewar jam'iyyarsa ta ɗanɗani kuɗarta:

"Masu zaɓe su ne suka tsayar da shawara kuma wannan sakamakon ya zama tamkar wata mummunar rana ga 'yan Social Democrats a nan Jamus. Babu wata rufa-rufa da za a yi a nan. Wannan mummunan kaye ne, bayan ƙaƙƙarfan yaƙin neman zaɓen da muka gudanar inda na lura da cikakken goya-baya daga jama'a a duk inda muka ya da zango."

Deutschland Bundestagswahlen 2009 SPD Pressekonferenz Frank-Walter Steinmeier

Steinmeier bayan kayen da jam´iyarsa ta sha a zaɓe

Steinmeier ya ƙara da yin nuni da cewar nuna halin sanin ya kamata a yanzu shi ne a yi ƙoƙari wajen sake ɗora jam'iyyar SPD kan wata hanya madaidaiciya.

"Alhakin dake kanmu a halin yanzu shi ne mu sake maidowa da SPD tsofuwar martabarta da sake ƙarfafa matsayinta. Ni kuma a nawa ɓangaren zai ba da cikakkiyar gudummawa ta, a matsayina na ɗan-adawa a majalisar dokoki ta Bundestag."

A nata ɓangaren shugabar gwamnati Angela Merkel ta bayyana matuƙar farin cikinta a game da sakamakon zaɓen, wanda ta ce ya zo daidai da abin da 'yan Christian Union suka yi fatan cimmawa na kafa sabuwar gwamnatin haɗin guiwa da jam'iyyar Free Democrats, ko da yake su ma 'yan Christian Union sun samu mummunan koma baya da ba su taɓa shaida irinsa ba tun bayan kafa tarayyar Jamus a shekara ta 1949.

Deutschland Bundestagswahlen 2009 CDU Angela Merkel

Merkel a cikin murnar lashe zaɓe

" Mun cimma kyakkyawar nasara. Mun cimma burinmu game da wannan zaɓe. Ina fatan zama shugabar gwamnatin dukkan Jamusawa domin kyautata makomar ƙasarmu, musamman a hali na rikicin da muke ciki yanzun. A tunani na dai muna iya ɗoki da murna a yanzun, kafin mu koma ga jan aikin dake gabanmu."

Shi ma shugaban jam'iyyar Free Democrats kuma babban ɗan takararta Guido Westerwelle ya tofa albarkacin bakinsa akan sakamakon zaɓen wanda ya bai wa jam'iyyarsa nasarar da bata taɓa samu ba a cikin tarihin tarayyar Jamus. Ya kuma fito fili ya nuna cewar jam'iyyarsa a shirye take ta shiga a dama da ita a sabuwar gwamnatin da za'a kafa.

"A shirye muke mu sghiga a dama damu a sabuwar gwamnatin da za a naɗa. Wannan sakamakon na ma'anar ɗaukar gagarumin alhaki bisa manufa."

Deutschland Bundestagswahlen 2009 FDP Guido Westerwelle

Shugaban FDP Guido Westerwelle

Sai dai kuma duk da murna da ɗoki da jam'iyyun Christian Union da Free Democrats ke yi da ma jam'iyyun Gurgzu da The Greens da suka samu gagarumar nasara, amma gaba ɗaya an sake fuskantar koma baya dangane da yawan masu kaɗa ƙuri'a, inda duka duka kashi 72 da rara cikin ɗari suka yi amfani da wannan dama, idan aka kwatanta da kashi 77 da rara cikin ɗari a zaɓen shekara ta 2005.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal