Martani kan sakamakon zaben Faransa | BATUTUWA | DW | 24.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Martani kan sakamakon zaben Faransa

Bayan kammala zagayen farko na zaben shugaban kasar Faransa, wanda ya bai wa 'yan takara biyu damar zuwa zagaye na biyu, 'yan kasar ta Faransa da ma sauran makwabtansu, na tofa albarkacin bakinsu.

Frankreich Präsidentschaftswahl Macron und Le Pen (Reuters/C. Hartmann)

'Yan takarar shugabancin kasar Faransa Emmanuel Macron da Marine Le Pen

'Yan takarar biyu wato Emmanuel Macron da Marine Le Pen dai, na da bambancin ra'ayoyi a kan batun kasancewar kasar ta Faransa a cikin kungiyar Tarayyar Turai. 'Yar takarar masu ra'ayin kyamar baki Marine Le Pen dai nada ra'ayin shirya zaben raba gardama a kan batun ci gaba da kasancewar Faransan cikin kungiyar ta EU da batun kudin bai daya na Euro da ma batun rufe kan iyakokin kasar ta Faransa ta yanhar ficewa daga tsarin iyakoki na bai daya na shengen, shi kuwa Emmanuel Macron na goyon bayan ci gaba da kasancewar kasar cikin Tarayyar Turan wato EU, sai dai yana ganin akwai bukatar kawo wasu sauye-sauye ga tafiyar kungiyar. A yayin da ya ke magana a gaban dubban magoya bayansa Macron ya ce akwai babban kalubale a gabansu:

Kalubale ga al'ummar Faransa

"Kalubalen da ke a gabanmu daga yanzu ba wai na kaje ka yi zabe ga wannan ko ga wancan ba ne, kalubale ne na ganin kowa ya jajirce don ganin cewa an kawo karshen wadan nan tsofaffin jam'iyyu da suka dade suna mulki a kasa tun shekaru fiye da 30, ba tare da sun kawo sauyin da 'yan kasa ke bukata ba, a kuma bude sabon babin siyasar kasarmu ta Faransa, ta re da yin yadda ko wane dan kasa zai samu matsayinsa a nan Faransa da kuma Tarayyar Turai wannan shi ne kalubalen da ke gabanmu."

Ma'aikatan hukumar zabe na aikin kidaya kuri'u bayan zaben Faransa

Ma'aikatan hukumar zabe na aikin kidaya kuri'u bayan zaben Faransa

A nata bengare 'yar takara Marine Le Pen kira ta yi ga 'yan kasar ta Faransa masu kishin kasa da su tashi tsaye domin bata goyon baya na ganin ta cika burin da ta sa a gaba na 'yanto kasar da ta ce tana cikin mawuyacin hali:

"Lokaci ya yi da zamu 'yanto 'yan kasar Faransa daga hannun 'yan takara da masu girman kai da suka hana ruwa gudu shekara da shekaru da suke son nuna wa Faransa hanyar da za ta bi, lalle ne a yanzu na kasance 'yar takarar al'umma. Ina kira ga duk masu kishin kasarmu da gaskiya daga duk inda suke, koma wa suka zaba a zagaye na farko, da su bi bayana a wannan kokawa ta zagaye na biyu. Ina kiransu da su yi watsi da cece-kucen da ba zai kaimu ko'ina ba domin burina shi ne na abun da zai kai kasar Faransa gaba."

Zabe ne da ya shafi nahiyar Turai

Daga ciki da wajen kasar ta Faransa dai akwai ra'ayoyi mabambanta dangane da zaben da kuma yadda suke kallon 'yan takarar.A nan Jamus ministan harkokin wajen kasar Sigmar Gabriel ya nunar da cewa zaben kasar ta Faransa batu ne da suke bi sau da kafa domin batu ne da ya shafi Turai baki daya. Su ma dai 'yan kasar Beljiyam da ke makwabtaka ta kut da kut da Faransa na ganin cewa zaben ya ba da mamaki ganin cewa manyan jam'iyyun kasar ne suka saba lashe zabuka a Faransan. A ranar bakwai ga watan Mayu mai zuwa ne dai za a je zagaye na biyu na zaben kasar ta Faransa, wanda ake ganin duk da cewa akwai alamar taron dangi kan 'yar takarar jam'iyyar masu tsatsauran ra'ayi, amma kalubalen da za a iya fuskanta shi ne, da dama daga wadanda suka yi zabe a zagaye na farko da wuya su sake yi a zagaye na biyu.

 

Sauti da bidiyo akan labarin