1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan rahoton HRW kan kisan 'yan Shi'a a Najeriya

Ubale Musa/GATDecember 23, 2015

Kungiyar Human Right Watch mai fafutukar kare hakkin bil adama ta nemi kaddamar da bincike mai zaman kansa da nufin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru a kisan da sojin Najeriya suka yi wa 'yan Shi'a a Zaria.

https://p.dw.com/p/1HSVY
Nigeria 2014 Selbstmordanschlag trauernde Schiiten
Hoto: Getty Images/AFP

A yayin da har ya zuwa yanzu kura ta kasa lafawa game da artabun da ya kai ga kisan daruruwan mabiya darikar Shi'a, Kungiyar Human Right Watch mai fafutukar kare hakkin bil adama ta nemi kaddamar da bincike mai zaman kansa da nufin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.

An dai dauki lokaci ana kace-nace an kuma kai har ga nunin yatsa a tsakanin kungiya ta 'yan uwa na Musulmi ko 'yan Shi'a da kuma rundunar sojan Najeriya bisa abin da ya faru a birnin zazzau makonni biyu baya.A tsakanin mutun bakwai zuwa dari takwas ne dai ake jin sun kai ga hallaka sakamakon fito na fito a tsakani na bangarorin biyu, abin kuma da ya tada hankali da martani mai zafi ciki dama wajen kasar.

Human Right Watch ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa

Nigeria Schiitische Muslime in Kano
Hoto: A. Abubakar/AFP/Getty Images

Na baya-baya a ciki na zaman Kuniyar Human Right Watch mai fafutukar kare hakkin bil adama da ta ce kisan bashi da hujja sannan kuma ta nemi kaddamar da bincike 'yantacce kai.

Wata sanarwar kungiyar dai ta ce binciken ya kaita har ga hira da wadanda suka ganewa idanunsu hargitsin na Zaria, ta ce soja sun yi harbi kan 'ya'ya na kungiyar a wurare har guda uku a cikin kwanaki biyu. Abun kuma da kungiyar ta ce ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 300.

Babban daraktan kungiyar dake kula da nahiyar Afirka Daniel Bakele dai ya nemi gwamnatin ta Abuja da tsayar da abin da kungiyar ta kira al'adar sojan kasan ta kisan da ba shi da gaira.

Sabon matsayin da ya zo kasa da awoyi 24 da nadin wani kwamiti na mutane biyar da nufin binciken bisa kisan a bangare na hukumar kare hakkin bil'adama ta kasar dai na nuna alamar dawowa daga rakiyar hujjar sojan da suka ce sun yi harbin ne a bisa kokari na kare kansu.

Kungiyoyin farar hula na nuna shakku kan tabbatar a gaskiya kan batun

Nigeria Soldaten
Hoto: -/AFP/Getty Images

Duk da cewar dai babu musu ga asarar ran dai rundunar sojan ne dai ke neman hukumar bin bahasin kokari na hallaka shugabanta a hannu na kungiyar , abun kuma da a cewar Dr Garba Umar kari da ke sharhi kan lamuran tsaro da siyasa ya sanya da kamar wuya hukumar tai tasiri wajen tabbatar da gaskiyar da 'yan kasar ke son su ji yanzu.

Bincike na hukuma ko kuma kokarin rufe baki, har ya zuwa yanzu dai fadar gwamnatin kasar ta Aso rock na cigaba a karatun na mujiya a cikin kisan da ya dauki fassara daban-daban cikin kasar.

To sai dai kuma a tunanin ministan tsaron kasar Janar Mansur Mohammed Dan Ali sun natsu da nufin zurin ido ga matakin jihar Kaduna da ke da ruwa da tsaki da neman baki na zaren

Abin jira a gani dai na zaman mafitar rikicin da ke zaman sabuwar barazana ga kasar da ke neman fita da kyar cikin rikicin yakin Boko Haram.