Martani kan haramta shigo da motoci ta kan iyakar Najeriya | Siyasa | DW | 06.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan haramta shigo da motoci ta kan iyakar Najeriya

Dokar haramta shigo da motoci ta kan iyakokin Najeriya zata fara aiki daga shekara mai zuwa, wanda hakan ya janyo mayar da martanin fargabar matakin ka iya shafar daukacin al'ummar kasar.

Daukar wannan mataki dai ya zo bagatatan ga mutanen da dama a Tarayyar ta Najeriya duk da cewa shekaru biyar kenan ana  a yi ba a yi ba a kan batun na masu shigo da motocin, wadanda ke tattaunawa da majalisar dattawa da ma gwamnati a kan bukatar a jinkirta. An dai dauki shekaru aru-aru al'ummar Najeriyar na shigo da motoci ta kan iyakokin kasa na kasa, irin su Benin da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Togo, inda a yanzu gwamnatin ta ce dasakel akan wannan tsari da take hangen zai taimaka mata wajen bunkasa hanyar kudaden shigarta.

Tuni dai kungiyar masu shigo da motocin ta Najeriya ta mai da martani akan wannan sabuwar doka da zata fara aiki daga ranar daya ga watan Janairu na shekara mai zuwa ta 2017, tana mai cewa wannan karawa gyambo fami ne daga koma bayan da sana'ar ke fuskanta, wanda tuni ta jefa mambobinsu dubu 250 cikin zama na kashe wando. 

Dubban ‘yan kasar ne dai ke cikin wannan harka ta shigo da motoci kasar ta kan iyakokin Najeriyar na kasa, inda wadannan yankuna suka zama cibiyar hada-hadar kasuwanci, da kai tsaye ke tasiri ga al'ummun kasashen. Sanin cewa Najeriyar na shigo da miliyoyin motoci a shekara abin tambayar shi ne: Ko tashoshin ruwanta zasu iya karbar kari na motocin da za'a shigo da su? 

Najeriyar dai ta dade ta na gwagwarmaya na ganin ta rage dogaro da shigo da motoci daga kasashen waje ta hanyar kerawa ko har hada su a cikin kasar, abinda ya sha fuskantar kalubale. 

Sauti da bidiyo akan labarin