Martani game da Hare-haren Bam a Najeriya | Labarai | DW | 01.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martani game da Hare-haren Bam a Najeriya

Ƙungiyar MEND ta ce ba ta yi niyyar kashe farar hula ba, ta yi nufin ta aika wa Goodluck Jonathan da saƙo ne

default

Motoci a wurin da bam ya tashi

Ƙasashe sun fara mai da martani dangane da harin bama-baman da aka kai a Abuja, babban birni  Najeriya, a yayin da ake paretin bukin cika shekaru 50 da samun 'yancin Kai daga Birtaniya. Ministan kula da harkokin wajen Birtaniya William Hague da kuma kantomar kula da harkokin wajen Ƙungiyar Tarayyar Turai Catherina Ashton, sun fitar da sanarwa inda suka yi Allah wadai da alamarin kuma suka aika da ta'aziyyar su ga iyalan wadanda wannan ta'asar ta shafa.

To sai dai ƙungiyar Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND), wadda ta ɗauki  alhakin hare-haren, ta ce da farko ta dasa bama-baman ne a dandalin Eagle Square, inda shugaba Goodluck Jonathan ya yi jawabi, kuma tayi gargaɗin cewa ta bada minti 30 domin mutane su bar dandalin kafin bama-baman su fashe. Ta kuma ƙara da cewa ba ta yi niyyar kashe farar hula ko ɗaya ba, amma ta yi nufin aika wa shugaba Goodluck Jonathan da saƙo, cewa babu wani dalilin kashe maƙuddan kudin da aka yi na wannan bukin cika shekaru 50, saboda gwamnati bata taka rawar gani ba.

Wadansu da suka gane wa idonsu abinda ya faru, sun shaida wa kamfanin dillancin labaru na Jamus cewa, motocin daukar marasa lafiya sun ɗauke gawarwaki guda 15 kuma wasu gawarwakin na kwance a inda bama-baman suka tashi, kana mutane da dama sun jikkata. 

Tuni dai shugaba Goodluck ya yi Allah wadai da wannan lamarin. A wata sanarwar da ofishin sa ya fitar, ya ja'jantawa iyalan mamatan, kuma ya yi alƙawarin cewa zaa kama duk waɗanda suka aikata wannan laifin, tare da hukunta su yadda ya kamata.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu