1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martani ga wasiƙar Paparoma

Taɓargazar da ta shafi cocin Katholika a Ireland na ci-gaba da ɗaukar hankalin jama´a

default

Paparoma Benedikt na 16

Ana ci-gaba da mayar da martani iri daban daban dangane da wasiƙar neman afuwa da Paparoma Benedikt na 16 ya aikewa waɗanda lamarin nan na lalata da ƙananan yara ya shafa a cocin Katholika na Janhuriyar Ireland. Bishop Bishop na Ireland sun yi maraba da wasiƙar a matsayin wata dama ta buɗe sabon babi ga cocin a ƙasar. To sai dai ƙungiyar waɗanda aka ci zarafinsu ta soki Paparoma da rashin taɓo ainihin wannan abin kunya wato manufar cocin ta kare waɗanda suka aikata laifin cin zarafin yaran.

To sai dai a nasa ɓangaren shugaban ɗarikar Katholika a Jamus Robert Zollitsch ya yi nuni da cewa wasiƙar neman gafarar ta shafi mabiya ɗarikar Katholika a tarayyar ta Jamus, inda a nan ma ake zargin wasu limaman cocin da yin lalata da ƙananan yara. Zollitsch wanda yake mayar da martani ga zargin kare wani lamarin cin zarafin da ya auku a cocinsa dake garin Oberhamersbach, ya yi watsi da wannan zargi. Ya ce har yanzu wannan lamarin na damunsa ƙwarai da gaske.

"Bisa bayanan da muka tattara ya zuwa yanzu da kuma la´akari da nauyin dake kai na a matsayin Archbishop, zan yi amfani da ƙa´idojin da taron bishop bishop na shekarar 2002 ya zayyana. Zan yi duk iya ƙoƙarin nemo shaidu da kuma waɗanda lamarin ya shafa."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala