1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani ga kisan al-Zarqawi

YAHAYA AHMEDJune 8, 2006

Bayan an tabbatad da mutuwar shugaban ƙungiyar al-Qaedan nan na Iraqi, Abu Musab al-Zarqawi, shugabannin ƙasashen Yamma sun yi ta mai da maratni kan labarin.

https://p.dw.com/p/Btzo
Abu Musab al-Zarqawi, wanda aka kashe a Iraqi.
Abu Musab al-Zarqawi, wanda aka kashe a Iraqi.Hoto: AP

Abin da da farko ake gani kamar raɗe-raɗi dai ya tabbata. Ƙungiyar al-Qaeda ta Iraqi, ta tabbatad da mutuwar shugabanta, Abu Musab al-Zarqawi, wanda dakarun Amirka suka kashe jiya daddare, a wani harin jiragen sama da suka kai a maɓuyarsa da ke wajen garin Baquba. Babban kwamandan rundunar sojin Amirkan a Iraqi, Janar George CASEY, ya bayyana cewa, ban da al-Zarqawin, wani babban mai ba shi shawara, Sheikh Abdel Rahman, shi ma ya gamu da ajalinsa a harin.

Firamiyan Iraqi, Nuri al-Maliki ne ya fara ba da sanarwar mutuwar al-Zarqwawin a cikin wani jawabin da ya yi wa ’yan ƙasarsa a kan talabijin, inda ya ƙara da cewa, masu kare lafiyarsa da ’yan hannun damarsa su 7, su ma sun sheƙa lahira a harin da dakarun Amirka suka kai musu, jiya daddare. Tuni dai Hukumar rundunar sojin Amirkan ta buga hotunan gawar al-Zarqawin, da na harin da aka kai a kan maɓuyarsa. A cikin jawabinsa, Firamiya al-Maliki, ya bayyana cewa:-

„Wannan dai wani kashedi ne ga duk wanda ya sa kisa da ɓarna a gabansa, da ya sake tunani, ya janye daga bin wannan manufar kafin aski ya zo masa a gaban goshi. Mun dai ɗau niyyar fatattakar duk ’yan tawaye har zuwa ramin kurarsu. Kafofin siyasarmu da jami’an tsaronmu za su ci gaba da wannan faufutukar har sai an cim ma nasara“.

Shugaban Amirka, George W. Bush, shi ma ya mai da martani ga labarin kisan Zarqawin. Da yake yi wa maneman labarai jawabi a fadar White House yau, George Bush ya bayyana cewa:-

„Jiya daddare, dakarun Amirka sun kashe ɗan ta’addan nan Al-Zarqawi. Kusan ƙarfe 6 da kwata na yamma agogon Bagadaza ne, dakarun ƙundumbalarmu, bisa wasu labaran jami’an leƙen asiri daga suka samu daga ’yan Iraqin, suka iya gano maɓuyarsa. Sa’annnan kuma suka nuna adalci ga babban ɗan ta’addar da aka fi nema a Iraqin.“

Shugaba Bush dai, bai yi wata wata ba, wajen bayyyana farin cikinsa da wannnan labarin. Ya ce wannan dai wani babban kaye ne ga ƙungiyar al-Qaeda, kuma wata gagarumar nasara ce ga yunƙurin da ake yi na yaƙan ta’addanci. To sai dai murnar shugaba Bush ɗin ba mai ɗorewa ba ce, kamar yadda shugaban ya tabbatar:-

„Zarqawi ya mutu, amma har ila yau za mu ci gaba da mawuyacin ɗaukin da muke yi a Iraqi. Muna sa ran ’yan ta’adda da ’yan tawayen, za su ci gaba da gwagwarmayarsu, duk da rashinsa. Kazalika kuma, tashe-tashen hankulla tsakanin jama’ar ƙasar ma za su ci gaba. Amma duk da haka, aƙidar ta’addanci ta yi asarar ɗaya daga cikin muhimman shugabanninta.“

Firamiyan Birtaniya Tony Blair, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa a kan labarin mutuwar al-Zarqawin. A wani taron maneman labarai a birnin London, Tony Blair, ya bayyana cewa:-

„Mutuwar al-Zarqawi, wani babban rauni ne ga kungiyar al-Qaeda a Iraqi, kuma wato cikas ne ga al-Qaedan a ko’ina ma. Amma bai kamata mu bari hakan ya yaudare mu ba. Mun san cewa, za su ci gaba da yin kisa, mun san kuma cewa akwai shingaye da dama da ya kamata mu kau da su. Amma su ma sun san cewa, mun lashi takobin sai mun fatattake su gaba ɗaya.“

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, shi ma ya yi jawabi game da kisan al-Zarqawin, inda ya bayyana cewa, mutuwar shugabanal-Qaedan a Iraqi dai, wato wani sauƙi ne ga ƙasar. Amma ba da ita za a kawo ƙarshen tashe-tashen hankulla ba.

A halin yanzu dai, manyan hafsoshin rundunar sojin Amirka a Iraqin, bisa cewar wani kakakinsu, Manjo Janar William Caldwell, na hasashen cewa wani ɗan ƙasar Masar, mai suna Abu al-Masri ne zai gaji al-Zarqawin.