Martani akan kalaman paparoma | Labarai | DW | 18.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martani akan kalaman paparoma

Pakistan tayi kira ga hukumar kare hakkin jamaa ta mdd ,dasuyi mahawara kann bukatar nuna sassaucin raayin addini,adaidai lokacinda kasashen duniya ke mayar da martani dangane da kalaman shugaban Darikar katholika ,paparoma Benedictnas 16,inda ya soki lamirin addinin islama.

Jakadan Pakistan Masood Khan,ya fadawa wakilan hukumar 47,kasarsa ta amince da nadaman da Paparoman yayi,sai dai kalaman nasa na danganta addinin Islama da tarzoma,batu ne dabai dace ba ko kadan.Mr Khan yace kaklaman na shugaban Darikar katholika,ya harzuka alummar musulmi dake sassa daban daban na duniya.Adangane da hakane jakadan Pakistan din,ya bukaci hukumar kare hakkin jamaar data ajiye rana guda a wannan makon domin tattauna batutuwan da suka shafi addini.

A garin Basra dake Iraki dai an gudanar da zanga zanga ,inda aka kone mutun mutumin paparoman.Ayayindas anan jamus kuwa majalisar musulmi ta kasar tayi kira ga fadar paparoman ,data tattauna da shugabannin musulmi ,dangane da zamantakewar addini.

 • Kwanan wata 18.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5Q
 • Kwanan wata 18.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5Q