1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani a kan harin rundunar tsaron Isra´ila a Jericho

March 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4w

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya bayyana matuƙar takaici, ga harin da dakarun Isra´ila su ka kai jiya, a gidan kurkukun Jericho, inda su ka yi awan gaba, da wasu pirsinoni da su ke zargi da aikata ta´adanci.

Shugaba Abbas, ya ce wannan hari, babban ta´adanci ne,wanda ƙarara, ya nuna halin reni, da wulaƙanci, da yahudawa ke wa al´ummomin Palestinu.

Kazalika, wannan hari, paƙat!!! ya rusa duk sauran yarjejniyoyin samar da zaman lahia, da aka rataba hannu a kai, tsakanin Israela da Palestinu.

A yayin da ya ziyarci gidan kurkukun Jericho, a ranar yau laraba,Mahamud Abbas, yace har abada, ba za su taɓa amincewa ba da wannan cin mutunci.

A ƙasashen dunia, an fara Allah wadai, ga gwamnatin Isra´ila, da kuma, kame kamen yan ƙasashen ƙetare a Palestinu.

Shugaban ƙungiyar gamayya Turai, Chanceller Wolfgang Schüssel, ya kiri ɓangarorin 2, da su dakatar da dukan take taken, da kan iya, ida gurbata yanayin yankin gabas ta tsakiya.

Ya kuma buƙaci, hukumomin Palestinu, su ɗauki matakan kariya, ga yan asulin ƙasashen ketare.

A wata mahaura da aka gudanar yau, a ƙungiyar gamayya turai, wakilai sun bayyana damuwa da halin da ke ciki a yankin gabas ta tsakiya.

A wannan mahaura, Martin Schulz, ɗan majalisar EU, daga ɓangaren jam´iyun gurguzu na mai