Martani a game da tazarcen Bachard Al Assad | Labarai | DW | 30.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martani a game da tazarcen Bachard Al Assad

Hukumomin Damascus, sun maida martani, ga huruncin gwamnatin Amurika a game da tazarcen shugaba Bashar Al-Assad.

Idan dai ba manta ba, a jiya ne, opishin ministan cinkin gida, ya bayyana gagaramar nasara da Al-Assad ya samu ta zarcewa, a kan kan karagar mulki, har tsawan shekaru 7 tare da kussan 98 bisa 100, na yawan ƙuri´un da aka jefa.

Bayyana wannan sakamako ke da wuya, gwamnatin Amurika, ta danganta shi da shirme, domin a cewar ta, ba a zaɓen demokraɗiya da ɗan takara ɗaya tilo, sannan kuma ya lashe kussan kashi 100 bisa 100, na ƙuri´un da aka kaɗa.

A martanin da ta maida, gwamnatin Syria, ta soki Amurika da yi mata shiga sharo ba shanu, a harakokin ta na cikin gida.