Maroko ta amince da bankunan Islama | Labarai | DW | 04.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maroko ta amince da bankunan Islama

Cikin bankunan da za a fara aiwatar da tsarin na bankin Islama a cikinsu akwai babban bankin nan na Attijariwaf da ke da alaka da gidan sarautar Maroko.

Kasar Maroko ta kasance kasa mai mafi rinjaye na Musulmi a baya-bayan nan da ta amince da kafa bankunan Musulinci, abin da ke zuwa bayan da a kasar a ke samun karuwar wadanda ke son amfanin da bankunan masu bin tsari na Shari'ar Islama.

Babban bankin kasar ta Maroko ya bayyana a wannan mako cewa ya amince da kafa irin wadannan bankuna guda biyar a wani bangare na cika alkawarin shekarar 2011 da jam'iyyar Islama ta  PJD mai kwance da wasu wajen kafa gwamnatin kasar ta bayyana.

Cikin bankunan da za a fara aiwatar da tsarin na bankin Islama a cikinsu akwai babban bankin nan na Attijariwaf da ke da alaka da gidan sarautar Maroko da Banque Centrale Populaire  da bankin BMCE mai zaman kansa , bankuna masu karfi a wannan kasa, sauran su ne bankin CIH da Credit Agricoledu Maroc. Bankuna hudu cikin wadannan za su yi aiki tare da bankunan na Moroko da cibiyar kula da hada-hadar kudi ta kasashen yankin Gulf, kamar yadda babban bankin kasar ya bayyana.