Maroko na neman zama memba a Kungiyar ECOWAS | Labarai | DW | 25.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maroko na neman zama memba a Kungiyar ECOWAS

Bayan da ta samu dawowa a babban gida na Kungiyar Tarayyar Afirka, sabon burin da kasar Moroko ta sa wa gaba, shi ne na kasancewa memba a kungiyar habbaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta CEDEAO ko ECOWAS.

Äthiopien Mohammed VI König von Marokko (Getty Images/AFP/Z. Abubeker)

Sarki Mohammed na shida na Maroko a lokacin taron kungiyar Tarayyar Afirka

Wata sanarwa ce dai ta ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Moroko ta sanar da wannan labari, inda tuni kasar ta tuntubi shugbar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf da ke a matsayin shugabar kungiyar ta ECOWAS kan wannan aniyya. A 'yan watannin baya-bayan nan dai kasar ta Moroko ta rubunya sumame na diflomasiyya a cikin kasashe da dama na Afirka, inda shugaban kasar da kanshi Sarki Mohammed na shida ya kai ziyara a kasashe da dama, tare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi daba-daban. A 'yan kwanakin baya-bayan nan ma dai Sakin na Maroko ya ziyarci kasashen Ghana, Zambiya da kuma kasar Guinea. Kuma a cewar hukumomin na Maroko, shigarta cikin Kungiyar ta ECOWAS, za ta kara karfafa kyaukyawar huldar da ke tsakaninta da kasashe membobin kungiyar.