Mari le Pen za ta fuskanci shari'a
March 2, 2017Talla
Kotu a kasar Faransa ita ta bukaci majalisar da ta cire rigar kariyar 'yar siyasar sakamakon yadda ta ce an sameta da laifin watsa wasu bidiyo na kisan jama'ar da 'yan Kungiyar IS suke yi a shafinta na Twitter a shekarar bara.A cikin watan Afrilu na shekara ta 2016 wani alkalin mai gudanar da bincike ya gayaceta domin ya saureta a kan wannan batu amma ta ki ammsa kira kan cewar tana da rigar kariya.