Maraba da yarjejeniyar zaman lafiya a Cote d´Ivoire | Labarai | DW | 06.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maraba da yarjejeniyar zaman lafiya a Cote d´Ivoire

Sakataren majalisar ɗinkin duniya Ban Ki-moon da shugaban hukumar haɗin kan Afrika Alfa Omar Konare, sun yaba da yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanyawa hannu tsakanin shugaban ƙasar Ivory Coast Laurent Ggagbo da babban madugun adawa Guillaume Soro. Yarjejeniyar ta buƙaci kafa gwamnatin wucin gadi da gudanar da zaɓe cikin watanni goma da kwance damara tare kuma da kawar da shigayen da aka shata na tsagaita wuta wanda ya raba yankin gabashi da kuma yammacin ƙasar. A halin da ake ciki dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya da sojojin Faransa sune ke tsaron waɗannan iyakoki. Ƙasar ta Ivory Coast ta rabu biyu bayan wani juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 2002.