Manyan malaman Islama sun amince da bayanan Paparoma
October 14, 2006Talla
Manyan malaman Islama daga ko-ina cikin duniya sun amince da bayanin da Paparoma Benedict na 16 yayi game da furuncinsa na sukar addinin Islama a wani jawabi da yayi a birnin Regensburg wanda ya sha tofin Allah tsine daga kasashen musulmi. Malaman sun nunar da haka a cikin wata budaddiyar wasika da suka aikewa mujallar islama ta Islamica Magazin wadda zata fita gobe a birnin Los Angeles na kasar Amirka. Wadanda suka sanya hannu kan wasikar sun ce sun amince cewar furucin da paparoman yayi ba ra´ayin kansa ba ne kuma ba ya nuna matsayin sa game da addinin na Islama. Daga cikin wadanda suka sanyawa wasikar hannu har da babban limamin ´yan shi´a na Iran Ayatollah Muhammad Ali Taskhiri da manyan malamai na kasashen Masar da Turkiya.