Manyan madatsun ruwa na Afirka
Afirka tana cikin wuraren da ake da manyan madatsun ruwa na duniya cikin kogunan Nilu da Kwango da kuma kogin Neja. Ga wasu daga ciki.
Babbar madatsar ruwan Habasha
Babbar madatsar ruwan Habasha ke kan gaba wajen girma a nahiyar Afirka. Wannan madatsar ruwa na yankin kudu maso yammacin kasar cikin kogin Nilu. An fara ginawa a shekara ta 2011 kuma yanzu haka madatsar ruwan na samar da hasken wutar lantarki mai karfin megawatt 6,000.
Madatsar ruwan Aswan da ke Masar
Madatsar tana garin Aswan da ke kudancin kasar Masar. Tana wuri mai girman murabba'in kilomita 169 na tafkin. Tana samar da hasken lantarki kimanin megawatt 2,100. An shafe shekaru 11 ana ginawa inda aka bude a shekarar 1971. Wannan madatsar ruwa da ke Masar ke zama ta biyu wajen gima a Afirka.
Madatsar ruwan Cahora-Bassa da ke Mozambik
Daya daga cikin manyan madatsun ruwa na duniya na a kasar Mozambik. Cahora-Bassa na da karfin samar da hasken wutar lantarki megawatt 2,075 da ke bin ta Aswan da ke Masar wajen karfi. Galibin wutar daga wannan madatsar ruwa ana turawa zuwa Afirka ta Kudu. Amma saboda zagon kasa lokacin yakin basasa a shekarar 1981 an gaza samar da wutar lantarki na tsawon shekaru 10.
Madatsar ruwan Gibe na III da ke Habasha
Wannan madatsar ruwa na da nisan kilomita 350 a yammacin birnin Addis Ababa fadar gwamnatin Habasha kuma tana cikin manyan ayyuka da aka gudanar. Madatsar ruwan Gibe na III a gaba daya za ta iya samar da hasken lantarki megawatt 1,870. An shafe kusan shekaru tara ana gina wannan madatsar ruwa inda kashi 60 cikin 100 na kudaden suka fito daga bankin Exim Bank na China.
Madatsun ruwan Inga da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango
Inga ya kunshi madatsun ruwa biyu: Inga ta I na samar da hasken wutar lantarki megawatt 351 sannan Inga ta II na samar da megawatt 1,424. An kaddamar da ta farko a shekarar 1972, ta biyu kuma a shekarar 1982 cikin tsarin samar da ci-gaba da ya gaza kai labari na tsohon shugaba dan kama karya Mobutu Sese Seko. Ana amfani da kashi 50 cikin 100 na karfin madatsun saboda rashin kula.
Madatsun ruwan Inga da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango
Madatsun ruwan biyu suna kusa da kogin Kwango. Gwamnatin kasar tana shirin kaddamar da madatsar ruwan Ingi ta III da za ta lakume kimanin kudin Euro biliyan 13, domin samar da hasken lantarki megawatt 4,800. Gaba daya idan aka kammala madatsun za su kasance wadanda suka fi karfin samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka baki daya.
Madatsar ruwan Akosombo da ke Ghana
Wannan madatsar ruwan Akosombo ta yi suna. Madatsar ruwan na yankin Tafkin Volta, wanda yake wuri mai girman da ya kai murabba'in kilomita 8,502. Madatsar ruwan tana samar da hasken wutar lantarki megawatt 921 sannan tana zama hanyar rage ambaliyar ruwa. Tafkin Volta na kuma zama wata hanyar da ta yi suna bisa kasuwanci.
Madatsar ruwan Kainji da ke Najeriya
Wannan madatsar ruwan na kogin Neja, kuma madatsar ruwan Kainji na cikin wadanda suka fi girma. Madatsar ruwan Kainji na da tsawon mita 65 kuma na samar da hasken wutar lantarki mai karfin megawatt 760. Wani bangaren kogin na zama hanya. An gina cikin shekaru hudu tare da kaddamar da madatsar a shekarar 1968.
Madatsar ruwan Tekeze da ke Habasha
Madatsar ruwan Tekeze na cikin manyan madatsun ruwa. Madatsar na cikin yankunan Amhara da Tigray da tsawon mita 188 mafi tsawo cikin nahiyar Afirka kuma na samar da hasken wutar lantarki mai karfin megawatt 300. An kaddamar a shekara ta 2009.
Madatsar ruwan Bujagali da ke Yuganda
Madatsar ruwan Bujagali ta kogin Nilu da ya wuce ta Yuganda kusa da Tafkin Victoria na samar da hasken lantarki megawatt 250. Madatsar ruwan na aiki tun shekara ta 2012 kuma babbar hanyar samar da wutar lantarki ta hanyar madatsun ruwa a Yuganda. Gina sabbin madatsun ruwa na Karuma da Isimba zai sauya haka, sai dai wannan zai janyo matsugunai ga dubban manoma domin kariya daga ambaliyar ruwa.