Manyan kasashe shida sun tattauna kan sanyawa Iran takunkumi | Labarai | DW | 07.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manyan kasashe shida sun tattauna kan sanyawa Iran takunkumi

Manyan kasashe 6 a duniya sun amince su tattauna game da yiwuwar sanya Iran takunkumi saboda kin da ta yi na dakatar da shirinta na nukiliya. A lokaci daya kuma kasashen sun ce a shirye suke su fara tattaunawa da gwamnati a Teheran. Iran dai ta ki aiki da wa´adin 31 ga watan agusta da kwamitin sulhu ya ba ta na dakatar da shirin inganta sinadarin uranium. Kasashen yamma na zarginta da shirin kera makaman nukiliya, duk da cewa kasar ta sha nanata cewa shirin na ta na samar da makamashi ne a hanyoyin lumana. Bayan tattaunawar da ta yi da ministoci daga Amirka, Faransa, Jamus, Rasha da kuma China, sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Margaret Beckett ta ce sun nuna takaicin su game da wani rahoto da babban jami´in diplomasiyar KTT Javier Solana ya bayar cewa shawarwarin da ya shafe watanni 4 yana yi da Iran ba su haifar da da mai ido ba. Amirka da Birtaniya na neman a dauki matakan jan kunnen Iran, yayin da Rasha da China ke son a nuna mata sassauci.