Manyan kasashe biyar na MDD za su yi taro domin daukar matsayi guda akan kasar Iran
January 26, 2006Talla
Ministocin kasashe dake da wakilcin dundundun a majalisar dinkin duniya, a mako mai zuwa idan Allah ya kai mu zasu gudanar da taro a birnin London domin shawarta matakin da zasu dauka na gaba a game da takadamar Nukiliyar kasar Iran da yaki ci yaki cinyewa.
Wani jamiín harkokin waje na kasar Britaniya wanda ya bukaci kada a baiyana sunan sa, yace ministocin kasashen biyar dake kujerar dundundun a majalisar dinkin duniya wadanda suka hada da Britaniya da Faransa da Rasha da China da kuma Amurka bugu da kari tare da kasar Jamus zasu tattauna a daura da taron gidauniya domin tallafawa kasar Afgahnistan don yanke shawarar da ta dace a game da takadamar Nukiliyar ta kasar Iran .