Manyan fafatawar Muhammad Ali
Muhammad Ali ya kafa tarihi ta hanyoyi da dama da suka hada da lashe kambun zakaran damben duniya sau biyu bayan rasawa. A kan hanya ya kafa tahiri da damben "rumble in the jungle" da kuma "thrilla in Manilla."
Nasarar gasar Olympic
Yana da shekaru 18 Cassius Clay (na biyu daga dama) tare da zinare da ya lashe a ajin masu matsakaicin nauyi lokacin gasar guje-guje da tsalle-tsalle a birnin Rom na Italiya. "Na gama gajiya ina son wasan ya kawo karshe." A cewar abokin karawarsa Zbigniew Pietrzykowski, wanda jini ya lullube masa fuska a zagaye na uku, kamar yadda yake tunawa. Clay ya zama gwani cikin wannan shekara.
Babban jarumi
Lokacin da Muhammad Ali ya lashe gasar farko na damben aji masu nauyi, ya kewaye wajen gasar yana cewa "Ni ne babban jarumi." Mafi yawan wadanda suka halarci wasan sun yi masa dariya lokacin, daga baya babu wanda yake tantama a kai, ya samar wa kansa matsayi ya zama "jarumin dan dambe na kowane lokaci."
Dokewa a zagayen farko
Ali ya fuskanci Liston a farkon kare kambunsa. Ya doke abokin karawarsa mai yawan shekaru cikin hanzari, ya kai Liston kasa mintoci biyu da fara wasa a zagayen farko. "Tashi mana" Ali ya ce masa. Sai dai an dakatar da wasan jim kadan da haka.
Taran aradu da ka
Clay ya kasance mai magana ta suka kafin gasar damben ajin masu nauyi na 1964, lokacin da ya fuskanci Sonny Liston. Wanda ya kalubalance shi ya yi alkawarin doke shi cikin kamar yadda ya nunar zuwa zagaye na takwas. Sai dai haka ya kasance a zagaye na shida. Liston ya ce ya samu rauni a kafada. A wannan shekara, Clay ya sauya suna zuwa Muhammad Ali.
Kar a maimaita
Ali ya bayyana karawa da dan wasan Jamus ta Yamma Karl Mildenberger a birnin Frankfurt a shekarar 1966, inda ya kare kambunsa na shida, a matsayin fafatawa mai zafi tun da ya zama zakara. Ali ya lashe bayan alkalin wasa ya tsayar da su a zagaye na 12 saboda rauni a idon Mildenberger. Ali ya ce baya fata ya sake fafatawa da dan wasan na Jamus ta Yamma.
Shan kayi na karni
A karon farko tun da ya zama kwararre Ali ya sha kayi a hannun Joe Frazier a dandalin birnin New York a shekarar 1971. Frazier ya doke Ali a zagaye na 15 bisa hukuncin duk alkalan. 'Yan wasan biyu sun samu kudaden da suka kai dala miliyan biyu da rabi kowanne a wasan da ake kira "fada na karni."
Zagaye bakwai na tsokana
A 1974, Ali ya kudiri sake cin kambun, inda ya fuskanci zakaran wannan lokaci George Foreman a Kinshasa. Ali ya shiga wasan a matsayin na baya domin Foreman daya ne a cikin masu naushi mai tsanani. Ali ya yi ta rawa har zagaye na bakwai yana karbar naushi daga zakaran, yana kuma tsokanar shi a tsawon lokacin.
Dokewa a zagaye na takwas
Nan da nan Ali ya shiga fafatawa tare da rugurguza Foreman, wasan da ake kira "rumble in the jungle" bayan zagaye na takwas. An yi wasan a birnin Kinshasa na Zayya da yanzu ake kira Kongo. Ali ya sake samun kambunsa na ajin masu nauyi a karo na biyu.
Nasara a Pilipin
Masana harkokin dambe suna ganin fafatawa tsakanin Ali da Joe Frazier a Pilipin a shekarar 1975 a matsayin gagarumin gasa. Duk 'yan wasan biyu an gwada gazawarsu lokacin gasar da ake kira "thrilla in Manilla. Alkalin wasan ya tsayar da gasar ana zagaye na 14 kuma Ali yana kan gaba da maki saboda Frazier ya samu rauni a fuska lokacin da yake kare naushi daga Ali.
Sarkakiyar kokuwa
A shekarar 1976 Ali ya zubar da kimarsa cikin wani hali saboda ya amince ya yi wasa da kwararren dan wasan kokuwa na kasar Japan Antonio Inoki. Inoki ya shafe tsawon wasan yana neman kama kafar Ali. Sannan Ali ya shafe lokaci yana neman kai masa naushi. Wasan ya kare cikin wani yanayi a zagaye na 15 babu wanda ya yi nasara.
Rasa kambu da sake dawowa
A shekarar 1978 Ali ya yi kuskuren raina abokin karawarsa, Leon Spinks. Lokacin neman kambun ajin masu nauyi Ali bai tsaya ya samu horo sosai ba, ya kuma rasa kambun. A wasan da aka sake cikin shekarar, Ali ya sake zama zakaran damben duniya karo na uku tare da bayyana yin ritaya daga wasan. Bai yi nasara ba a yunkurin sake dawowa.
Tsaffin abokan gaba
Bayan ritaya, Ali ya zama aboki ga mutanen da suka fi yin adawa da juna lokacin wasan dambe, Joe Frazier da George Foreman.