1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofin taimakon raya kasa na Faransa da Jamus

Umaru AliyuJanuary 23, 2008

Kungiyoyin taimakon raya kasa na Faransa da Jamus, sun gudanar da taro a Bonn domin nazarin manufofin su na taimakon raya kasashe masu tasowa, musamman na Afrika.

https://p.dw.com/p/CwJb
Tsohon shugaban gwamnatin Jamus, Konrad AdenauerHoto: AP


Ranar Litinin aka cika shekaru shekaru 45, tun da Konrad Adenauer da Charles de Gaulle suka sanya hannu kan yarjejeniyar abokantaka a fadar Elysee, tsakanin Jamus da Faransa. A ƙoƙarin girmama wannan rana, wakilan ƙungiyar Red Cross ta Faransa da ƙungiyar Welthungerhilfe da ƙungiyar raya ƙasa daga Jamus suka gudanar da wani taro na haɗin gwiwa a nan Bonn. Al'amuran da suka tattauna kansu a lokacin taron, ba sun shafi abokantaka ne kawai tsakanin ƙasashen biyu ba, amma sun kuma duba yadda zasu kyautata dangantakar ƙasashen biyu da sauran kasashen ketare. Mahalarta taron sun yi nazarin yadda zasu haɗa gwiwa, domin taimakawa matsayin rayuwa a ƙasashe masu tasowa, musmaman na Afrika da yadda matasa zasu iya bada gudummuwar su a wannan ƙoƙari. Umaru Aliyu yana dauke da ƙarin bayani.


A Faransa da kuma a nan Jamus, yanzu haka akwai ƙungiyoyin agaji masu tarin yawa dake shigar da matasa a manufofin su na aiyukan taimakon raya ƙasa. Ƙungiyar taimakon raya kasa ta Jamus, wato DED a taƙaice, ta tanadi wani shiri, wanda a ƙarƙashin sa, matasa sukan sami sami damar musayar ra'ayoyi ta fuskar al'adu da koyon sana'oi, ta hanyar aiyukan taimakon raya kasa a ketare. Günter Kosngen yayi ƙarin bayani a game da wnanan shiri da aka sanya masa suna Weltwärts:


Yace a lokaci guda, burin mu shine mu bada gudummuwa ga aiyukan ƙungiyoyi dake haɗin kai damu, mu kuma baiwa matasa damar sake shiga al'amuran yau da kullum a kasashen su, idan suka komo gida daga aiyukan da suka yi na tamakon raya ƙasa a ƙetare, yadda matasa zasu ƙara fahimtar yanayin zaman tare da da fahimtar al'adun abokan zaman su da kuma fahimtar halin zama, tsakanin ƙasashen su na asali da ƙasashe masu tasowa. Wannan yana ɗaya daga cikin mauhimman manufofin shirin na Weltwärts.


Ƙoƙarin ƙara bunƙasa manufar cuɗanyar al'adu, shine babban burin shirin shirin da Faransa ta gabatar mai suna Generation et Cooperation. Tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin agaji na Jamus, ko wace shekara akan tura ɗan Faransa ɗaya tare da ma'aikacin raya ƙasa na Jamus zuwa wata ƙasa ta Afrika. Har ma yar Faransa, Anne Marie Euzen tace wannan manufa ana iya kwatanta ta a matsayin haɗin kai tsakanin ƙasashe ukku, saboda mazauna ƙasashen na Afrika sune musamman sukan yanke ƙudiri a game da inda aka fi buƙatar taimakon raya ƙasa da akan basu.


Dalibi Martin Schramm ya tabbatar da haka, bayan da ya komo gida daga taimakon raya ƙasa da ya bayar na gina wani asibiti a Burkina Faso.


Yace wannan dai kyakkyawan tsari ne na cuɗeni-in-cuɗeka. Mune muka zo da kuɗin da ake buƙata, amma su suka nuna mana inda zamu gina dakin na shan magani, yadda shike shugabancin aikin ginin ya kasance a hannun su kansu yan Burkina Faso, kuma ana iya cewar mu ma'aikatan Burkina ɗin ne kawai.


Matasan ƙasashen biyu sun fahimci cewar aiyukan su a ƙasashe masu tasowa basu tsaya kawai ga samun ƙwarewa da fahimtar matsayin rayuwa da al'adun wasu ƙasashe na ƙetare ba. Amma burin al'amarin gaba ɗaya, shine ƙoƙarin kyautata matsayin rayuwa a ƙasashen masu tasowa. Anna Christina Meyer, ma'aikaciyar ƙungiyar raya ƙasa ta Jamus, take cewa:


Da farko mutum yakan rika hangen yadda nahiyar Afirka take, to amma a bisa duba na biyu mutum yakan fahimci cewar wajibi ne a ɗauki nahiyar yadda take a zahiri. Wato ba mutum ya rika mafarkin yadda Afirkan take ba, amma ya gane yadda take a haƙiƙa. Afirka dai ba ƙasa ce guda ɗaya ba, amma nahiya ce kamar sauran nahiyoyi, ɗauke da ɗimbin jama'a da ƙabilu da ɗabi'u dabam dabam da tarihi mai yawan gaske. Wannan kuwa abu ne mai ban sha'awa.