Manufofin MDD dangane da karni na 21 | Siyasa | DW | 13.09.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin MDD dangane da karni na 21

Kasashen afurka na fama da tafiyar hawainiya wajen cimma manufofin MDD dangane da karni na 21

Manufofin na MDD dangane da karni na 21 sun hada da yaki da matsalar talauci da sassauta radadin cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro da kuma bunkasa al’amuran ilimi. Sai dai kuma a yayinda ake samun kyakkyawan ci gaba a kasashen kudu-maso-gabacin Asiya da kudancin Amurka, su kasashen Afurka sai fama suke da tafiyar hawainiya, inda suka wayu gari tamkar ‚yan rakiya ne kawai, ba ma dangane da manufofin na majalisar dinkin duniya ba, har ma a game da tattaunawar da wakilai zasu yi a zauren taron kolin majalisar a cikin kwanaki uku masu zuwa hade da sanarwar bayan taron da za a bayar. A karkashin kudurin da MDDr ta cimma a misalin shekaru biyar da suka wuce an yi fatan shawo kann yawan matalauta ‚yan rabbana ka wadatamu da misalin kashi 50% nan da shekara ta 2015 da dakatar da kashi biyu bisa uku na mace-machen yara da kuma ba da ilimi ga kowa-da-kowa. Sai kuma tabbatar da hakkin mutane na samun ruwan sha mai tsafta da muhallin zama. Amma a wannan halin da muke ciki yanzun kasashen Afurka bakar fata sune cimma wannan buri zai ta’azzara akansu idan an kwatanta da irin ci gaban da ake samu a sauran sassa na kasashe masu tasowa, kamar yadda bankin raya kasashen Afurka ya nunar a cikin rahotonsa. Duka-duka kasashe goma daga cikin kasashen Afurka bakar fata su 48 ake kyautata zaton zasu iya cimma manufofin na MDD akan wa’adin da aka tsayar na shekara ta 2015. Daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu kuwa har da rashin nagartattun hanyoyin sadarwa da rashin iya gudanarwa da kuma rashin wata kyakkyawar niyya daga bangaren masu riko da madafun mulki a kasashen Afurka da lamarin ya shafa. Babban misali a nan shi ne yadda aka yi wa matsalar yunwar nan da ta rutsa da kasar Nijer rikon sakainar kashi, inda magabatan kasar suka ki amincewa da mawuyacin halin da jama’a ke ciki ballantana su dauki nagartattun matakan da suka dace wajen shawo kann lamarin. Kazalika wasu daga cikin kasashen na fama da bunkasar yawan jama’a ba kakkautawa a yayinda a daya bangaren suke fuskantar koma bayan yawan amfanin da suke nomawa kuma a sakamakon haka suka dogara kacokam akan taimako daga ketare. Alkaluma sun nuna cewar yara ‚yan kasa da shekaru biyar da haifuwa kimanin miliyan 11 kann yi asarar rayukansu galibi a kasashen Afurka a duk shekara sakamakon wasu cututtukan da ba su gagari magani ba. Kazalika yaduwar cutar kanjamau na barazana ga makomar kasashe da dama na wannan nahiya, inda a wasu kasashenta, duk da bunkasar tattalin arzikin da suke samu, amma a daya bangaren suke samun karuwar yawan ‚yan rabbana ka wadata mu. Wani muhimmin abin da zai taimaka kasashen na Afurka su haye tudun natsira shi ne, kasashe masu ci gaban masana’antu su cika alkawururrukansu na bunkasa yawan kudadensu na taimakon raya kasa, duk da dagewar da kasar Amurka take wajen ganin lalle sai an soke wannan manufar dake kunshe a cikin kudurin sanarwar bayan taro.