Manufofin MDD dangane da karni na 21 | Siyasa | DW | 24.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin MDD dangane da karni na 21

Har yau ana fama da tafiyar hawainiya a game da manufofin MDD dangane da karni na 21

Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya

A lokacin wani taron da aka gudanar a nan birnin Bonn dangane da bikin samun shekaru 60 da kafa MDD, wakiliyar majalisar akan manufofin nata na raya makomar kasashe masu tasowa Eveline Herfkens ta bayyana kwarin guiwar cewa kwalliya zata mayar da kudin sabulu akan manufa. Ta kuma yi kira ga dukkan kasashe masu ci gaban masana’antu da masu tasowa da su nuna halin sanin ya kamata wajen rungumar nauyin dake kansu. Ta kuma kara da cewar:

Ana da ikon cimma wadannan manufofin, ko shakka babu. Mun san matsalolin dake akwai, kuma muna da ikon magance su. Abu daya dake hana ruwa gudu shi ne wata cikakkiyar azama daga bangaren jami’an siyasa. Wadannan tabbatattun manufofi ne da ake fatan cimmusu, amma ba kawai maganganu na fatar baki ba.

Tun dai abin da ya kama daga shekara ta 2002 tsofuwar ministar taimakon raya kasashe masu tasowan ta kasar Netherlands take taimaka wa sakatare janar na MDD Kofi Annan wajen hada kann matakan da ake dauka domin cimma wadannan manufofin da suka hada da yaki da talauci da ba da ilimin faramare ga kowa da kowa da daga matsayin mata da kyautata kiwon lafiya tare da murkushe cututtuka irinsu AIDS da zazzabin cizon sauro da suka zame wa dan-Adam kayar kifi a wuya. To sai dai kuma har ya zuwa halin da muke ciki yanzun babu wata alamar dake nuna cewar kwalliya zata mayar da kudin sabulu kafin wa’adin da aka tsayar na shekara ta 2015. Dangane da maganar kayyade yawan masu fama da matsalar talauci zuwa kashi 50% dai MDD na kann hanyar cimma nasara sakamakon ci gaban da kasar China ke samu. To sai dai kuma ita kanta Eveline Herfkens ta hakikance cewar ba za a iya daukar ci gaban na kasar China a matsayin mizanin cimma nasarar manufar ta murkushe matsalar talauci ba. Ta ce a dai wannan marra da muke ciki yanzun babu wani takamaiman matakin da za a iya cewar shi ne zai taimaka a shawo kann matsalar talauci. Bugu da kari kuma ainifin dukkan matsalolin na da dangantaka da juna. Misali maganar ba da ilimin faramare ga kowa-da-kowa, a nan ba za a samu nasara ba, matsawar da ba a samu kafar dakatar da yawan mace-machen mata ba, inda za a wayi gari ‚ya’ya mata ne ke daukar nauyin kula da kannensu. A wasu kasashe masu tasowan ma sai mata sun yi tafiya mai nisa kafin su debo ruwan sha mai tsafta. Muddin ba a samu kafar shawo kann ire-iren wadannan matsaloli ba to kuwa da wuya a cimma biyan bukata a game da manufofin da MDDr ta sa a gaba dangane da sabon karnin nan na 21 da muke ciki yanzun.