Manufofin gwamnatin Isra′ila tsohon yayi ne | Siyasa | DW | 21.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin gwamnatin Isra'ila tsohon yayi ne

'Yan siyasar Jamus sun yi tir ga matakin Isra'ila na hana 'yan siyasar ƙetare kai ziyara Gaza

default

Avi Primor tsohon jakadan Isra'ila a Jamus

Isra'ila ta sha suka da kakkausan lafazi daga 'yan siyasar Jamus kuma manyan ƙawayenta bayan da ta hana ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel, izinin kai ziyara Zirin Gaza domin duba ayyukan da Jamus ke gudanarwar a yankin. To sai dai ga Avi Primor tsohon jakadan Isra'ila a Jamus kuma mai adawa da takunkumin Isra'ila akan Gaza ya ce wannan matakin ba akan ministan kaɗai ya ke aiki ba.

A wata hira da aka yi da shi Avi Primor tsohon jakadan Isra'ila a Jamus wanda yanzu yake shugabanr cibiyar nazarin manufofin ƙasashe Turai a jami'ar Herzliya ta Isra'ila ya yi ƙarin bayani yadda a Isra'ila aka ɗauki sukan da ministan raya ƙasashen masu tasowa na Jamus Dirk Niebel yayi da kuma muhauwarar da ta biyo baya.

"Tun ba yau ba Isra'la ke shan suka daga kowane ɓangare. Na fahimci ministan Niebel amma a hannu ɗaya ya kamata a san cewa ya samu kansa ne a cikin wani mataki da ya shafi kowane dan siyasa na duniya, da a ba a son su shiga Zirin Gaza domin Isra'ila na ganin haka tamkar marawa ƙungiyar Hamas ne."

Shi dai ministan na Jamus wanda ke zaman babban abokin Isra'ila ya kai ziyarar yini huɗu a ƙasar ta Yahudun Isra'ila inda daga nan ya so zuwa Zirin Gaza domin duba ayyukan raya ƙasa da Jamus ke yi a Zirin na Gaza. Ba shi ne wani ɗan siyasar ƙetare da Isra'ila ta hana shi shiga Gaza ba. A kan haka Avi Primor ya ce a lokuta da dama gwamnatin Isra'ila tana tabƙa wasu kurakurai da dama musamman akan manufofinta. Ya ce yana ganin waɗannan manufofin sun zama tsohon yayi kuma kuskure ne duk da cewa ta shafi kowane ɗan siyasa amma ba Niebel kaɗai ba. Yanzu haka dai gwamnati ta sauƙaƙa takunkumanta akan Gaza, amma ta makara, inji Primor sannan sai ya ƙara da cewa.

"Akwai wasu abubuwan dake shige mana duhu. Yanzu ana magana game da canza manufofi kan Gaza. Wai shin me yasa aka jira har sai bayan bala'in da auku na jiragen ruwan agaji ga Gaza? Me yasa sai bayan matsin lambva daga Amirka sannan aka canza wannan manufa ta rashin adalci a ciki gwamnatinmu? Ba wanda zai iya fahimtar abin da ke faruwa."

A ranar shida ga watan Yuli Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai gana da shugaban Amirka Barack Obama a fadar White House inda ake sa rai shugaban na Amirka zai ƙara matsa ƙaimi domin Isra'ila ta sauƙaƙa matakan ƙuntatawa al'umar Zirin Gaza. Avi Primor dai na mai ra'ayin cewa Amirka za ta taka muhimmiyar rawa bisa manufa.

"Amirka na da babban angizo. Ba za mu iya taɓuka wani abu ba sai da taimakonta. Amirka za ta iya matsa mana lamba ta kowane fanni domin mun dogara kanta kacokan. Idan ta ga dama tana iya yin duk abin da ta so akanmu."

To sai dai tambaya a nan ita ce ko Amirkar za ta yi amfani da wannan ikon na ta akan Isra'ila?

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal