Manufofin Amurka akan yaƙi da ayyukan Tarzoma | Siyasa | DW | 11.09.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin Amurka akan yaƙi da ayyukan Tarzoma

Kokarin amurka na wanke fuskar ta a idanun Duniya, tun bayan harin 9/11

default

Barack Obama

Daraja da mutuncin Amurka ya faɗi a idanun Duniya sakamakon irin suka da tsohuwar gwamnatin George W. bush tasha, akan kurkun gwale-gwale na guantanamou, da Abu Ghraib, da kuma take haƙƙin jama'a, duk kuwa da suna yaƙi da ayyukan tarzoma.

Bayan hawan shi karagar mulki , shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana sabbin manufofinsa na ganin cewar dangantaka ta ingantu tsakanin Amurka da ƙasashen musulmi. Kamar yadda Direktan ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta ƙasa da ƙasa ta Human Rights Watch dake birnin Washinton Tom Malinowski yayi bayani.

" Yace, a jawabinsa a birnin Alkahira, shugaba Obama ya nuna alamun sabbin manufofinsa. Waɗanda suka haɗa da dangantaka ta kafaɗa da kafaɗa, da kuma tuntuɓan juna, idan aka fuskanci wani saɓani. Bai kamata ayi la'akari da duk wanda bai bi manufofin Amurka a matsayin abokin adawa ba. Duk batu ne daya danganci dawar da martabar Amurka"

Yaƙi da ayyukan tarzoma a ƙarkashin gwamnatin George W bush dai ya haifar da tauyewa mutane haƙƙokinsu. Kuma a bayyana take cewar gwamnatinsa bata darajawa hakkin bil'adama. A lokuta da dama an sha cafke mutane babu gaira babu dalili musamman waɗanda keda alaka da ƙasashen musulmi, ana jefa su a kurkuku tare da azabtar dasu ba tare da basu damar kare kansu.

Ƙungiyoyin kare hakkin jama'a kamar su Human Right watch sun sha kokawa dangane da wannan matsala ba tare da an kula su ba. Sai dai a ƙarkashin gwamnatin Barack Obama lamarin ya sauya inji Tom Malinowski..

" Yace, a yanzu babu azabtarwa ayayinda 'yan CIA ke yiwa mutum bincike,yanzu babu kurkukun azabtar da mutane na sirri. An dai sace mutane daga nahiyar turai ko kuma daga wasu ƙasashen duniya ana tura su zuwa kurkukun gwale-gwale domin azabtarwa"

Guantanamo detainees pray before dawn

Guantanamo

Kafa sansanin gwale gwale na Guantanamou da Amurka tayi bayan harin 11 ga satumba dai, ya zubar da mutuncin Amurka tare da janyo mata baƙin jini a idanun Duniya. Dangane da haka ne da hawansa karagar mulki, Barack Obama ya sanar da rufe sansanin a watan janairu. Sai dai acewar Direktan Human right Watch, ba sanarwa ba aiwatar da rufe sansanin yake da kamar wuya...

" Babbar matsalar itace, zartar da yadda za a yi da pursunoni guda 240 da tsohuwar gwamnatin daga gabata tayi watsi dasu a kurkukun. Kowa ya amince da cewar dukkan waɗanda aka samesu da laifin ta'addanci, za a iya zartar da hukunci akansu. Sai dai wasu na tsoron cewar zai kasance abu mawuyaci a zartar da hukunci akan wasu. Musamman dangane da cewar sakamakon azaba da suka sha, da wuya a samu wata shaida a kansu"

Kamata yayi dai dukkan mutanen da suka daɗe a tsare a sansanin Guantanamou kuma ba a samesu da wani laifi ba, a barsu su koma ƙasashen su na asali. Idan kuma hakan ba zai yiwu ba, abasu izinin komawa ƙasashen dake kawance da Amurka.

Guantanamo Flash-Galerie

Guantanamo

Gwamnatin Amurka na yanzu dai ta fahin cewar darajawa 'yancin bil adama shine tubalin tabbatar da zaman lafiyar ƙasar, inji mananazarci kan harkokin yankin gabas ta tsakiya na ƙungiyar POMED dake Washington, Andrew Albertson..

" Gwamnatin Obama tayi la'akari dacewar, a kokarin yaki da ayyukan tarzoma, kamar Alkaida, kokuma 'yan Taliban a Afganistan, ko kuma mayakan Iraki, abunda yafi muhimmanci shine , mu samarwa da mutane kariya. Ba za cimma nasara ba, har samun tabbatar da war da martaban mu na kare 'yancin jama'a"

A yanzu haka dai da yawa daga cikin Amurkawa na danganta matsalar tattalin arziki da ƙasar ta faɗa a yau da yake-yaken da Amurkan ta jagoranta a afganistan, Iraki, Kosovo, Bosnia dama sauran ƙasashe. Barack Obama dai yana cigaba da kira ga Amurka da su dada yin hakuri a kokarinsa na daidai sahun lamura, domin ba batu na hanzari ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammad

Edita: Mohammad Nasir awal