1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofin Amurka a Iraki

December 20, 2006
https://p.dw.com/p/BuX4

Fadar gwamnatin Amurka ta white house ta tabbatar dacewa shugaba George W Bush na laakari da da karin yawan dakarun sojin kasar a na karamin lokaci a kasar Iraki.A yanzu haka dai Amurkan nada dakarun ta dubu 140 a wannan kasa.A hiran da jaridu sukayxi dashi,shugaban na Amurka ya bayyana cewa zai fadad ayyukan dakarun tsaron ne domin kalubalantar ayyukan tarzoma na lokaci mai tsawo nan gaba.Tuni dai aka umurci sabon sakataren tsaro Robbert Gates da yayi nazarin lamarin.

Rahotanni daga irakin na nuni dacewa,da safiyar yau ne wani dan kunar bakin wake ya afkawa ayarin jamian yansanda da motarsa,inda ya kashe mutane 6 nan take,kana wasu 29 suka jikkata.Wannan harin ya auku ne a gunduwar Jadriya dake yankin kudu maso yammacin Bagadaza.