1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofin Amurka a Iraki

January 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuV2

A ranar larabar nan ne akesaran shugaba George W Bush na Amurka zai gabatar da sabbin manufofin kasarsa aIraki.A wannan tsarin dai anasaran Amurkan zata sanar da kara yawan dakarunta a wannan kasa na gajerten lokaci,da jamiai kimanin dubu 20.Yan majalisar dokokin daga jammiyar Democrats dai,tun da farko bazasu bashi damar karin dakaru aIrakin ba tare da adadi ba.Sabuwar kakakin majalisar dokokin kasar Nancy Pelosi daga jammiyar democrats dake da rinjaye yanzu a majalisar Amurkan,ta bayyana cewa dole shugaba Bush ya bada bayanan dukkan karin kudade da zaa kashe a kasar ta Iraki.A halin da ake ciki yanzu haka dai kasar ta Iraki na fama da karin tashe tashen hankula,inda ko ayau ma mutane 18 suka rasa rayukansu,baya ga masu yawa da suka jikkata.