Manufofin Amirka sun taimaka wajen karuwar ta´addanci a duniya | Labarai | DW | 09.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manufofin Amirka sun taimaka wajen karuwar ta´addanci a duniya

Tsohon jami´in dake kula da aikin yaki da ta´addanci na shugaban Amirka GWB, wato Richard Clarke ya ce gwamnatin Amirka ita ma tana da laifi game da karuwar ayyukan ta´addanci na masu matsanancin ra´ayin Islama. Lokacin da yake magana da jaridar Franfurter Rundschau gabanin cikar shekaru biyar da kai hare haren ranar 11 ga watan satumba, Clarke ya ce ra´ayin masana ya zo daya cewar tun bayan shekara ta 2001 hadarin fuskantar ayyukan ta´addanci ya karu. Ya ce hakan kuwa na da nasaba da yakin da Amirka ta kaddamar kan Iraqi. Ya ce yanzu haka dai Iraqi ta zama wani sansanin horas da ´yan ta´adda.