1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin ƙasashen yamma dangane da Afghanistan

Har yau tsugunar da sojojin ƙasashen yamma a Afghanistan bai tsinana kome ba

default

Rundunar ƙawance ta ISAF

Sojojin ƙasashen yamma dai a yanzu haka suna nan jibge a ƙasar Afghanistan, to amma ayar tambaya anan ita ce , ta yaya fatar da akeyi ta samun dai daituwar al'amuran siyasa zata samu, kuma wanan shine tunanin aksarin 'yan Afghanistan.

Ƙasashen yamma kansu basu san mi sukeyi ba , wannan shine tunanin Hayatullah Rafiq. Ko da yaushe idan ya kunna radion sa, yace sai dai ya ji bayanai masu karo da juna daga ƙasashen yamma. Wassu na cewa za su ƙara yawan dakarunsu wassu kuwa na cewa za su janye. Don haka malamin jami'ar ɗan shekaru 64 da haifuwa ya ce, ya rasa mi zai gaskanta a tsakanin waɗannan batutuwa. Manufar ƙasashen yamma da ta gwamnati a Afghanistan duk sun bi ruwa, sabo da haka Hayatullah Rafiqi ya bada wassu misalai.

"Anso a tura wani ɗan ƙasar Birtaniya ya kasance wakilin sakatare janar MDD na musamman a Afghanistan, to amma Karzai ya ƙi. Karzai ya ce wai Birtaniya tana son tattaunawa da Taliban don biyan buƙatunta ne kawai, kuma wannan ba Alheri bane ga Afghanistan. Yanzu sai gashi Karzai da kansa ya na son tattaunawa da Taliban, wannan ya na nunin cewa kowa buƙatarsa kawai ya sa a gaba. Amma wai duka ace ana yaƙi da 'yan ta'adda, ana neman tsaro, ana son sake gina ƙasa da buƙatu na musamman, waɗanda ba bu wanda ya san su"

Schule in PAGHMAN in der Provinz KAPISA, Afghanistan Kinderhilfe Afghanistan

Yara a ajin makaranta a Afghanistan

Mafiya yawan 'yan Afghanistan dai ba su da imanin ƙasashen da suke da dakaru a ƙasarsu, suna can ne domin biyan buƙatar mutanen Afghanistan, kamar yadda Muhammad Ibrahim Spesali wani mazaunin lardin Helmand ya ce.

"Amirka, da Jamus, da Kanada basa magana da baki ɗaya, ko wacce ƙasa da nata buƙantun ta zo nan,Waɗannan ƙasashen duka suna da kekkyawar dimokraɗiya da siyasar ƙetare, to amma kaito a Afghanistan kam sun kasa, domin yau su ce haka, gobe su ce wata daban"

Don haka Hayatullah Rafiqi, wanda ya tashi ya girma a gidansu dake lardin Kadahar, inda ya ke koyarwa a jami'a, ya ce batun yaƙi da 'yan ta'adda tatsuniya ce.

"Idan sojojin ƙasashen waje suna yaƙi don kawar da 'yan ta'adda. to tun shekarar da ta gabata batun 'yan ta'adda sai ƙararuwa yakiye. bawai a Afghanistan kaɗai ba, dubi abinda ke faruwa a Pakistan. to ina ake yaƙi da 'yan ta'ddan"

Yanzu dai ana ta bada ayoyin tambaya, shin da wace irin manufa ƙasashen yamma suka tura soji a Afghanistan, wane tsari sukayiwa ƙasar, dole ne kuwa su bada wannan amsar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmad Tijani Lawal