1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufar Taimakon Raya Ƙasa Ta Jamus

Tijani LawalOctober 28, 2009

Jamus ta naɗa sabon ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa

https://p.dw.com/p/KHeE
An sake naɗa Merkel kan muƙamin shugabar gwamnatin JamusHoto: AP

A yau ne aka ƙaddamar da bikin rantsar da sabuwar gwamnatin jamus ƙarƙashin shugabar gwamnati Angela Merkel. To sai dai kuma wani abin lura game da sabuwar gwamnatin ta haɗin guiwa shi ne yadda aka danƙa wa jam'iyyar Free Democrats ma'aikatar taimakon raya ƙasashe masu tasowa, wadda da farkon fari jam'iyyar ta nema da a rufe ta gaba ɗaya. To ko shin a yanzun za a samu canjin alƙibla dangane da manufofin taimakon raya ƙasa na Jamus.

Dirk Niebel Das neue Kabinett
Dirk Niebel, sabon ministan taimakon raya ƙasa na JamusHoto: picture-alliance / dpa

Shi dai tsofon sakatare janar na jam'iyyar Free Democrats Dirk Niebel, wanda aka danka wa ma'aikatar kawo yanzu babu wata rawa da ya taka a matsayin jami'an siyasar taimakon raya ƙasa. A maimakon haka an fi saninsa ne a matsayin ƙwararren masani akan harkar ƙodago da tattalin arziƙi. Kuma tun watan afrilun shekara ta 2005 aka naɗa Dirk Niebel sakatare-janar na jam'iyyar ta FDP, muƙamin da aka ce ya taka rawar gani wajen tafiyar da shi. Amma a yanzu an danƙa masa wata ma'aikata, wadda a lokacin yaƙin neman zaɓe jam'iyyar ta ce zata kawar da ita. Shugaban jam'iyyar The Greens, Jürgen Trittin ya zargi FDP da ƙokarin mayar da manufofin taimakon raya ƙasashe masu tasowa wata manufa ta tsumulmular kuɗi.

"Duk wanda ya dubi shawarwarin dab kuka bayar da kuma yadda kuke ƙoƙarin daidaita kasafin kuɗin ƙasa zaku ga cewar ma'aikatar taimakon raya ƙasa ita ce muhimmiyar kafar da kuke so ku yi tsumulmular kuɗi kanta. Kuma naɗa Niebel muƙamin ministan taimakon raya ƙasa da aka yi tamkar dai an ba wa kura ajiyan nama ke nan."

Johannes Vogel, shugaban reshen matasa na 'yan Democrats kuma wakili a majalisar dokoki ta Bundestag dake da shekaru 27 na haifuwa yayi fatali da wannan zargi, inda ya ce maganar soke taimako ga ƙasashe matalauta ba ta taso ba a tattaunawar da jam'iyyar FDP tayi. Ainihin ayar tambayar da ta saka ita ce ko shin abu ne da ya dace a ci gaba da taimaka wa ƙasashe masu matsakaicin ci gaban masana'antu kamar China da Indiya, waɗanda a haƙiƙa suke da ikon tura kumbon ɗan-Adam zuwa sararin samaniya. Sai kuma maganar ma'aikatar da ya kamata a haɗe ta da ma'aikatar taimakon raya ƙasar.

:"Ana iya saka wannan ayar tambayar, kuma mun tattauna wannan batu. Amma maganar ba ta shafi tsumulmular kuɗaɗen taimakon raya ƙasa ba. Sai dai maganar dake akwai ita ce, tun da yake wannan manufa wani ɓangare ne na manufofin ƙetare, shin ya cancanta a samu ma'aikatu biyu a wawware. A saboda haka muka ga abu mafi alheri shi ne haɗe ma'aikatun biyu ƙarƙashin tuta guda. Amma ba batu ake yi game da ƙayyade yawan taimakon da ake bayarwa ba. Bisa akasin haka."

A lokacin da ake gabatar da yarjejeniyar haɗin guiwa ta sabuwar gwamnatin ranar asabar da ta shige shugaban jam'iyyar FDP Guido Westerwelle ya sosa wa 'yan jarida zuciya inda yake cewar:

"Kamar dai wani ya fito fili ne ya ba da shawarar dakatar da taimakon raya ƙasa. Muhimmin abu a gare mu shi ne ba a tafiyar da wani ɓangare na manufofin ƙetare a ma'aikatar taimakon raya ƙasa ba. Wajibi ne su riƙa tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da juna."

Abin da 'yan jarida suka fahimta daga wannan lafazi na Westerwelle shi ne cewar, a matsayinsa na sabon ministan harkokin waje ba ya ƙaunar ganin wani ministan taimakon raya ƙasa da zai cimma nasara bisa manufa. An sha yin irin wannan zargin akan magabacinsa Frank-Walter Steinmeier, sakamakon nasarorin da tsofuwar ministar taimakon raya ƙasa kuma 'yar jam'iyyarsa ta SPD Heidemari Wieczorek-Zeul ta cimma bisa manufa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala