Manufar lafiya don cigaban ƙasashe masu tasowa | Labarai | DW | 23.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manufar lafiya don cigaban ƙasashe masu tasowa

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da P/M Britaniya Gordon Brown sun zayyana wani jadawalin sabbin shawarwari wanda duniya baki daya zata iya amfani da shi domin haɓaka kiwon lafiyar alúma a ƙasashe matalauta. Shugabanin biyu suka ce ana buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan cuttuka kamar HIV/AIDS da rage mace macen ƙananan yara da mata masu juna biyu a ƙasashe masu tasowa. Merkel da Brown sun ƙara da cewa zaá ƙaddamar da wannan sabon shirin ƙawancen ta ƙasa da ƙasa don inganta harkokin lafiya a ranar 5 ga watan Satumba mai kamawa, suka ce hakan zai kuma tabbatar da cewa agajin da ƙasashen ƙetare ke bayarwa sun isa kai tsaye ga bukatun lafiya na ƙasashe masu tasowa. Ƙawancen zai ƙunshi ƙasashen Britaniya da Jamus da Canada da Norway da bankin duniya da kuma ƙungiyar lafiya ta duniya.