Manufar Jamus da Faransa ta samar da ci-gaban EU
October 27, 2010Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta kare shawarar da Jamus da Faransa suka gabatar ta hukunta duk wata ƙasa ta Ƙungiyar Tarayyar Turai da za ta gaza cimma matsayin da ake buƙata daidai da yarjejeniyar samar da ɗorewar ci-gaban Tarayyar Turai. A cikin jawabin da ta yi ga majalisar dokoki a yau kafin Ƙungiyar Tarayyar Turai ta gudanar da taron kolinta a birnin Brussels a gobe Alhamis, Merkel ta ce Faransa da Jamus za su dage bisa aiwatar da tsaurara sharuɗa na aikin kuɗi ko da ma hakan zai buƙaci yin gyaran fuska ga yarjejniyar Lisbon da ke tafiyar da harkokin cikin gidan Tarayyar Turai. Shugaban hukumar zartarwar Ƙungiyar Tarayyar Turai, Jose Manuel Barroso ya yi wa ƙasashe mambobi tuni da cewar a taron na gobe za a mai da hankali ne akan hanyoyin samar da ci-gaban ƙungiyar. Tuni dai ƙungiyar ta fuskanci tsaiƙo game da wannan taro saboda adawar da wasu mambobin nata kamar ƙasar Luxembourg ke nunawa game da dakatar da haƙƙin kaɗa ƙuri'a ga duk wata ƙasa da za ta gaza cimma wannan matsayi.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal