Manufar EU game da gudun hijira | Siyasa | DW | 26.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufar EU game da gudun hijira

Taron ƙoli karo na uku tsakanin Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka a Libya

default

A ranakun 29 da 30 ga watan nan na Nuwamba shugabanni kimanin 80 daga ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai da takwarorinsu na Tarayyar Afirka za su gudanar da taron ƙoli karo na uku a Tripolis babban birnin ƙasar Libya. Hulɗar tattalin arziki tsakanin Turai da Afirka za ta kasance a samar jadawalin taron, amma za a kuma yi musayar yawu akan batutuwa kamar zaman lafiya, tsaro, sauyin yanayi, samar da abinci da kuma batun 'yan gudun hijira. Ƙasashen Turai dai sun ƙuduri aniyar shawo kan matsalar gudun hijira da gaggawa. A saboda haka suke ganin dacewar duk wani mataki da za su ɗauka don cimma wannan manufa, ciki har da ƙulla ƙawance da shugabannin kama karya kamar Muammar Ghaddafi.

Akwai makeken giɓi tsakanin faɗi da cikawa idan ana magana ne game da manufar 'yan gudun hijira ta nahiyar Turai. Masu faɗa a ji a hedkwatar ƙungiyar EU dake birnin Brussels da sauran manyan biranen ƙasashen EU ba sa gajiya wajen koyawa gwamnatocin wasu yankunan abubuwan da suka shafi haƙin ɗan Adam da mulki na doka. To sai dai ƙasashen EU kansu ba sa yi da wasa wajen tinkarar batun gudun hijira a kusa da su. Bayan wata ganawa da takwarorinsa a baya-bayan nan game da batun baƙin haure, an jiyo ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere yana cewa.

"Za mu iya amincewa da ci-gaba da bin al'adar taimakon jin ƙai a Turai a matsayin wata ƙasa mai karɓar 'yan gudun hijira, idan za mu iya faɗawa jama'a cewa za mu yaƙi masu fatali da wannan al'ada."

Ƙasashen kudancin Turai kamar Girika da Spain na ganin kamar sauran ƙawayensu na Turai sun ƙyale su su kaɗai su ji da matsalar dubban baƙin haure, saboda matsalar rashin zumunci mai ƙarfi da tsakanin ƙasashen Turan waɗanda ke fama da nauye nauye akansu.

Nauyin dake kan waɗannan ƙasashen na kudancin Turai na da nasaba da wasu tsare tsare, domin dokokin EU sun tilastawa ƙasa ɗaukar ɗan gudun hijirar da ya sanya ƙafarsa a cikin yankin Tarayyar Turai. Ƙasashe kamar Jamus za ta iya rayuwa da wannan doka. Duk da cewa jami'an hukumomin tsaron kan iyakokin Turai suna farautar 'yan gudun hijira domin hana su shigowa Turai amma hakan bai wadatar ba. Kimanin shekaru biyu da suka wuce EU ta fara tattaunawa da Libya game da wata yarjejeniya a asirce domin rage kwararowar 'yan gudun hijirar, kamar yadda wakiliyar jam'iyar The Greens a majalisar dokokin Turai Franziska Brander ta nunar.

"Fargabarmu ita ce ta haka EU za ta iya shawo kan matsalar gudun hijira sannan a sakawa Ghaddafi ta hanyar samun haɗakar tattalin arziki da EU, sauƙaƙa dokokin ba da visa ga 'yan Libya. Wannan ita ce fargabarmu."

Gwamnatin Italiya ta Firaminista Silvio Berlusconi ita ce ta farko wadda ta karɓi shugaban na Libya da hannu bibiyu sakamakon wani shiri na ba ni gishiri in ba ka manda, wato tsare 'yan gudun hijira a saka masa da dubban miliyoyin Euro. Kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterrez ya fusata da wannan shiri, yana mai nuna shakku cewa Libya ba za ta ba da cikakkiyar kariya ga sahihan masu neman mafakar siyasa ba.

"Ba ma jin cewa a Libya akwai kyakyawan yanayi da zai ba da damar samun cikakkiyar kariya ga waɗanda suka cancin samun mafakar siyasa."

A halin da ake ciki shugaban na Libya ya kori hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta Majalisar Ɗinkin Duniya daga ƙasar, kuma ba wanda ya san abin da ke faruwa ga 'yan gudun hijirar da aka koma da su ƙasar dake arewacin Afirka.

Mawallafa: Peter Heilbrunner/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar