Manufar Bush a kasar Iraqi | Labarai | DW | 08.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manufar Bush a kasar Iraqi

‘yan majalisa Democrat a birnin Washington sunyi gargadin cewar shugaba Bush zai sha wuya wajen kokarin san na neman goyan bayan majalisa a sabon manufar sa a game da kara lambar dakarun Amurka dake kasar Iraki. Duk da cewar Pentagon ta sanar cewar shugaba Bush zai yi jawabi akan manufar tasa cikin wannan makon, ‘yan majalisar Congress sunce lallai Bush na da aiki a gaban sa wajen shawo kansu inda yake bukatan bayyana musu dalila masu karfi da zai sa Amurka ta cigaba da kashin kudi wajen mamayan Iraki. Jaridar New York Times ta sanar jiya lahadi cewar shugaba Bush na da niyar kara tsugunar da karin sojojin yaki dubu 20 a birnin Bagadaza. A halin yanzu dai yawan sojin Amurka da suka mutu ya kai dubu 3 da Karin hudu da aka kasha a jiya lahadi a birnin Bagadaza.