1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maniyyata kusan miliyan biyu sun fara aikin hajjin bana

December 28, 2006
https://p.dw.com/p/BuW9

Rahotanni daga Saudia na nuni da cewa kusan mahajjata miliyan biyu ne a yanzu haka suka isa dutsen minna, don fara aikin hajjin bana gadan gadan.

Rahotanni daga kasa mai tsarki na nuni da cewa mahajjatan dake sanye da fararen kyalla, tun da sanyin safiyar yau ne suka fara wannan balaguro mai nisan kilomita biyar, daga gabashin birnin Makka.

Tuni dai gwamnatin Saudiya ta girke dubbannin jami´an tsaro a hanyoyin zuwa minnan, don tabbatar da tsaro da oda a yayin wannan aiki, kamar yadda wakilinmu Garba Ubale Danbatta ya shaida mana.