Manazarta sun ce Merkel ta lashe muhawara | Labarai | DW | 04.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manazarta sun ce Merkel ta lashe muhawara

Yayin da ya rage makonni uku a gudanar da babban zaben gama gari a nan Jamus, shugabar gwamnati Angela Merkel ta yi wa abokin hamaiyarta Martin Schulz nisa a matsayin wacce alamu ke nuna za ta lashe zabe

Manazarta al'amuran siyasa da ke tsokaci kan muhawarar da ta gudana tsakanin shugabar gwamnati Angela Merkel da abokin hamaiyarta Martin Schulz sun ce ba zai sauya akalar zaben ga dan takarar jam'iyyar adawa ba.

Masanin siyasa Michael Shpreng ya ce zai wuya yakin neman zaben shulz ya sauya lamura ko ra'ayin jama'a.

Ita kuwa mataimakiyar shugabar jam'iyyar CDU Julia Kloeckner cewa ta yi Merkel ta nuna bajinta da kwazo tare da kafa hujjoji a muhawararta.

Ministan shari'a kuma dan Jam'iyyar SPD Haiko Maas ya yabawa gwaninsa Martin Schulz wanda ya ce yana da manufa mai kyau ta harkokin waje.

A waje guda dai Angela Merkel da Martin Schulz sun baiyana ra'ayoyi mabambanta game da shigar Turkiyya kungiyar Tarayyar Turai.

Yayin da Martin Schulz yace zai dakatar da tattaunawar shigar Turkiyya kungiyar EU idan ya ci zabe, ita kuwa Angela Merkel cewa ta yi ba ta taba tunanin Turkiyya za ta shiga kungiyar ta EU ba.

Sauran batutuwan da shugabannin suka yi muhawara akan su sun hada da tsaro da 'yan gudun hijira da kuma yaki da tsattsauran akida.