1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Man fetir alheri ko akasin haka a Nijar

November 30, 2017

Wasu dai a kasar bayan shekaru shida da fara aikin hako man fetir na cewa kafa kamfanin mai SORAZ ci baya ne ga kasar saboda tsadar mai.

https://p.dw.com/p/2oYmo
Algerien Tiguentourine Gasfabrik Geiseldrama
Hoto: AP

Hakikan bayan kwashe shekaru shida da kafuwa a yankin Jihar Damagaram tare da fara aikin tatar mai gadan-gadan jama'a daga masu ababen hawa zuwa 'yan farar hula na ci gaba da bayyana ra'ayoyi game da ribar da suka ci ta mai da kuma kamfanin tace man kasar mai sunan SORAZ baki daya, sun ce dai ba su ga canji ba saboda tsada gara ma lokacin da ba a tace man.

Tun bayan kafuwar kamfanin tace man ne dai 'yan farar hular irin su MPCR suka fara gwagwarmayar ganin sai an rage farashi amma dai har yanzu babu ci gaba, ga gurbata muhalli.
A shekarun baya dai manyan motocin dakon mai na 'yan kasuwa ne da kuma gwamnati ke shigo da man daga ketare, su ma dai sun ce babu aiki, faduwa suke kawo yanzu. A na su waje kungiyoyin da ke sa ido a kan ma'adinai irin su GREEN na ganin dai har yanzu akwai sauran aiki kafin kaiwa ga nasara baki daya.

Symbolbild Pipeline in Algerien
Hoto: AP