Mali: Shirin wanzar da zaman lafiya na tangal-tangal | Siyasa | DW | 13.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mali: Shirin wanzar da zaman lafiya na tangal-tangal

Yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a bara tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a Mali na cin karo da kalubale. Har yanzu ba a kwance damarar mayakan sa kai ba.

Wani yanki na arewacin Mali musamman ma Kidal da kewaye na ci gaba da kasancewa a hannun kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai. Hasali ma dai tsaro ya sake tabarbarewa saboda rashin jibge sojoji a wannan yanki. Ko da a ranar Laraba da ta gabata, sai da wata motar dakarun Faransa da ke kiyaye zaman lafiya ta taka nakiya a kusa da garin Tessalit, lamarin da ya salwantar da rayukan uku daga cikinsu.

Yarjejeniya da gwamnati da 'yan tawaye suka rattaba hannu a kanta a ranar 15 ga wata Mayun 2015, ta tanadi karbe makamai daga hannun masu tayar da zaune tsaye, tare da sanyasu cikin rundunar sojin kasar ta Mali.

Sidi Zahabi Minister für nationale Versöhnung in Mali

"An aiwatar da wasu bangarori na yarjejeniya"- Zahabi Ould Sidi Mohamed

Sai dai minista Zahabi Ould Sidi Mohamed da ke kula da hadin kai da raya yankin arewacin kasar ta Mali ya ce duk da cewa suna cin karo da kalubale, amma akwai wasu matakan wannan yarjejeniya da suka yi nasarar aiwatarwa.

"Duk abubuwan da wannan yarjejeniya ta tanada an kafasu musamman ma kwamitin da zai zartas da yarjejeniyar, da kwamitin gaskiya da sasantawa. Amma dai mun yi latti matuka wajen tsugunar da 'yan bindiga da karbe makamansu, domin ya kamata a aiwatar da shi kwanaki 60 bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiyar."

Da sauran aiki don duba sauran batutuwa

Har yanzu ba zama ko da daya da aka yi da nufin sauran bahasi daga wadanda rikicin ya rutsa da su, ballanta ma a yi maganar yafiya ko garzayawa kotu don neman hakki. Amma Ousmane Oumarou Sidibé wanda shi ne shugaban hukumar gaskiya da sasanta rikicin na Mali ya nunar da cewa suna aiki tukura don ganin cewar sun sauke nauyin da ya rataya musu a wuya.

"Sasantawa za ta kasance sakamakon aikin bincike da bankado gaskiya da muke gudanarwa yanzu haka. Sannan muna neman hanyoyin hana sake afkuwar abin da ya faru a baya. Wannan yunkuri ne zai sa kowa ya kokarta yafe wa juna."

Al'ummar Mali sun zaku da ganin cewar rikicin da aka yi fama da shi a arewacin kasar ya zama tarihi.

Kawo karshen ayyukan tarzoma

Tuareg NMLA - Kämpfer im Norden von Mali

Mayakan NMLA a arewacin Mali

Ko da su ma membobin kungiyoyin fararen hula sai da suka ce dole ne gwamnati ta yi kokarin kawo karshen hare-haren ta'addanci da safarar miyagun kwayoyi da ake fama da su a arewacin Mali. Sidy Mohamed Adiawiakoye na daya daga cikinsu.

"Wannan yarjejeniyar da aka sa hannu a kanta kusan shekara guda ke nan tana tafiyar hawainiya. Bisa ga dukkanin alamu kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba matukar bangarorin da abin ya shafa ba su canja salon kamun ludayensu ba. Dole a hanzarta tsugunar da 'yan bindiga, saboda ta wannan hanya ce za a tantance wane ne dan tawaye, wane ne dan ta'adda, wane ne yake fada don cimma wata kyakkwayar manufa."

Gwamnatin ta Mali ta tsawaita dokar ta baci a duk fadin kasar da nufin hana jama'a zirga-zirga cikin dare. Lamarin da ke nuna cewar har yanzu da sauran rina a kaba dangane da batun tsaro.

Sauti da bidiyo akan labarin