Mali: Masu shirin kai hari a Bamako sun shiga hannu | Labarai | DW | 28.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: Masu shirin kai hari a Bamako sun shiga hannu

Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zagi da shirin kai wani sabon hari a birnin Bamako. An kama mutanen da wasu kayayyaki da ke nuni da hakan inji wata majiya ta tsaro a kasar ta Mali.

Harin dai an tsara kai shi ne tun yayin babban zaman taron kasar Faransa da kasashen Afirka da ya gudana a ranaikun 13 da 14 ga watan nan na Janairu, amma  kuma ta sabili da kwararan matakan tsaron da aka dauka a wurin taron hakan ba ta samu ba. Shi ya sa masu ikirarin Jihadin suka dage wannan danyan aiki na su har ya zuwa wani lokaci. Mutanen biyu dai da aka kama 'yan kasar ta Mali ne da aka haifa a yankin arewacin kasar, inda daya mai shekaru 29 an haife shi ne a birnin Gao, yayin da dayan kuma mai shekaru 21 a garin Intillit.