1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: Kammala yakin neman zaben kananan hukumomi

A wannan Juma'a ce (18.11.2016) aka kammala yakin neman zaben kananan hukumomi wanda zai gudana a ranar Lahadi a kasar Mali, wanda kuma shi ne na farko tun bayan zaben Shugaba Ibrahim Boubacar Keita a 2013.

Tsawon lokacin wannan yakin neman zaben, an sha fuskantar suka daga bangarori daban-daban tare da barazanar 'yan jihadin arewacin kasar. Duk da cewa akwai hotunan 'yan takara da kuma shirya wasu tarurrukan gangami, ana iya cewa wannan yakin neman zaben bai yi wani armashi ba a Bamako babban birnin kasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da za a yi zaben kananan hukumomi a kasar ta Mali tun bayan zaben Ibrahim Boubacar Keita a matsayin shugaban kasar ta Mali a watan Augusta na 2013, inda aka yi ta daga shi tun daga shekara ta 2014. A fadin kasar ma baki daya yakin neman zaben bai yi wani armashi ba, musaman ma a yankin arewacin kasar inda ake fuskantar barazana daga mayakan jihadi.