Mali: An kama bindigodi a jami'ar Bamako
December 21, 2017Talla
Rikicin dai ya samo tushe ne daga zaben magatakardan kungiyar daliban sashen ilimin kimiya da fasaha na jami'ar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alhamis din ma'aikatar ministan tsaro na kasar ta Mali ta ce dalibin da ya rasu, ya gamu da ajalin nasa ne a sakamakon harbin bindiga. Daga cikin makaman da 'yan sanda suka kama a jami'ar baya ga daliban 16, sun hada da kananan bindigogi masu sarrafa kansu kirar gargajiya guda 20 da harsashai 19 da adduna 63d da wukake 208 da sanduna shida.