1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: An fara shari'ar Janar Sanogo

A wannan Larabar ce wata kotu a Mali, ta fara sauraron shari'ar tsohon jagoran kifar da mulki janar Amadou Sanogo, a kan zargin sace mutane da aikata kisan gilla

 Shari'ar na zuwa ne shekaru uku da rabi bayan zargin gwamnatinsa ta soji da kisan gillar sojoji 21.

A watan Maris na 2012 ne dai Sanogo ya jagoranci kifar da gwamnati da ya yi sanadiyyar kifa rda gwamnatin tsohon shugaba Amadou Toumani Toure, wanda kuma ya jefa kasar cikin tashe-tashen hankula, da ya janyo 'yan tawayen Abzinawa da masu kishin addini karbe madafan ikon yankin arewaci.

Lauyansa ya ce "Na tabbata ba shi da laifi, ni ke kare janar Sanogo. Ina tabbatar da cewar bashi da laifi, abin da na ke kokarin bayyaawa ke nan. Kundin tsarin mulkin Mali da na kare hakin dan Adam sun nuna cewar, wanda ake tuhuma ba shi da laifi har sai kotu ta tabbatar da cewar ya aikata laifin. Don haka duk zargin da ake yi masa na kashe jama'a, ya zuwa yanzu a wurinmu kazafi ne kawai".

A ranar Juma'a biyu ga watan Disamba ne za'a ci-gaba da sauraron shari'ar ta Janar Sanogo da mukarrabansa, mutumin da aka cafke a watan Disamban 2013.