1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malesiya: Za a yi wa Anwar Ibrahim afuwa

Abdullahi Tanko Bala
May 11, 2018

Firaministan Malesiya Mahathir Mohammed ya tabbatar da cewa za a afuwa ga Anwar Ibrahim wanda ke tsare da shi bisa laifin Luwadi da kuma cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/2xWFi
Malaysien, Kuala Lumpur: Premierminister Anwar Ibrahim
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Sarkin Malesiya ya amince ya yi afuwa ga fitaccen dan siyasar kasar Anwar Ibrahim wanda ake tsare da shi.

Firaministan Malaysia Mahathir Mohammed ya sanar da hakan yayin da yake jawabi ga yan jarida.

Ana tsare da Anwar Ibrahim ne bisa laifin luwadi da kuma cin hanci da rashawa. Kuma ba zai rike kowane mukami ba har sai an yi masa afuwa.

 Mahathir ya kuma ce zai sanar da majalisar zartarwar gwamnatinsa mai mutum goma tare da baiyana sunayen ministoci a ranar Asabar.