1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malesiya: Mahathis zai zama Firaminista

Abdullahi Tanko Bala
May 10, 2018

Mahathis Mohammed mai shekaru 92 a duniya zai zama shugaban da aka zaba mafi tsufa a tarihi bayan da kawancen jam'iyyun adawa suka yi nasara a zaben Malesiya.

https://p.dw.com/p/2xTax
Malaysia Mahathir Mohamad
Hoto: AFP/Getty Images/M. Rasfan

Firaministan Malesiya Najib Razak ya amince da shan kaye a zaben gama gari da aka gudanar a ranar Laraba. A wani jawabi da ya yi Najib Razak yace ya amince da zabin al’ummar Malesiya. 

"Mun amince da zabin jama'a kuma jam'iyyar Barisan Nasional na kara jaddada kudirinta na martaba tafarkin dimokradiyya."

Najib ya kara da cewa sarkin Malesiya zai yanke hukunci akan wanda zai zama Firaminista na gaba kasancewar babu jam’iyyar da ta sami gagarumar rinjaye.

Kawancen jam’iyyun adawa karkashin jagorancin tsohon Firaministan kasar Mahathir Mohammed mai shekaru 92 sun sami mafi yawan kujeru a majalisar dokoki inda suka kayar da jam’iyyar Barisan Nasional wadda ta shafe kusan shekaru 60 ta na mulki tun bayan da kasar ta sami yancin kai.

Mahathir Mohammed yace yana sa ran za'a rantsar da shi Firaminista nan gaba a yau Alhamis.