1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi: Yaki da aurar da yara kanana

Ramatu Garba Baba
November 29, 2017

Gwamnatin kasar Malawi ta aiwatar da dokar hana auren wuri ga yara mata masu kananan shekaru. Kafin kafa wannan doka, ana iya aurar da yara mata kanana, muddin iyaye sun amince.

https://p.dw.com/p/2oSy6
Portugal, Lissabon, Zwangsheirat
Hoto: AMIC Bissau

 Enala Gondwe wata mai  fafutukar ganin an yaki jahilci da zummar bai wa yara mata dama na samun ilimi, ta kaddamar da shiri inda take bin lungu da sakon kasar tana wayar da kannun 'yan mata kan sanin mahinmancin ilimi.

Burin Enala Gondwe shi ne ta karfafawa yara mata gwiwa don ganin sun sami ilimin zamani koda a baya sun fuskanci matsaloli da suka hana su zuwa neman ilimi. Auren wuri da talauci ko jahilci a bangaren iyaye a cewarta na taka mahinmiyar rawa a koma bayan da ilimin mata ke fuskanta a Malawi.

Enala Ngulu Gondwe da ita kanta ta taba samun kanta cikin wannan matsala ganin an yi mata aure tana da shekaru 13 kacal, ta ce rana guda ta yanke shawarar komawa makaranata kuma bayan cimma burinta, ta ga ashe kuwa da bukatar wayarwa sauran yara mata kai don sanin mahinmancin ilimi.

A wannan lokacin ta kai ziyara a wata makaranta da ke a garin Karonga a arewacin kasar ta Malawi, acewarta tana fatan ganawa da daliban don basu labarin rayuwarta don kada su yi kasa a gwiwa.

Gondwe ta ce ta soma tunannin daukar mataki na yakar jahilci a tsakanin yara mata a can baya a lokacin da ta ke zaman aure ganin a wannan lokacin ma ta na iya daukar dawainiyar kula da kanta da kuma yaran ta 6, don kuwa mijin bai damu da bukatar ta ba balle na yaran ba.