Makon bunƙasa Noma a Afirka | NRS-Import | DW | 23.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Makon bunƙasa Noma a Afirka

Bunƙasa noma a Afirka na buƙatar tallafi ne mai ɗorewa amma ba gudunmawa na wucin gadi ba.

default

Yanayin gona a Afirka

Zaá iya shawo kan matsalar yunwa ne kawai a Afirka ta hanyar sabbin dabaru na fasahar zamani don inganta noma, a cewar Peter Michael Schmitz masanin kimiyyar albarkatun gona kuma wakili a majalisar bunƙasa ayyukan gona ta kasar Jamus.

Schmitz yace zai kasance abu mai alfanu idan zaá taimakawa Afirka da naurorin noma na zamani da kuma sabbin dabaru na kimiyya, domin akwai damuwa ga irin yadda fari da sauran ƙwari ke cinye kimanin kashi 30 cikin ɗari na amfanin da aka noma, saboda haka ana buƙatar Iri mai kyau da maganin kashe ƙwarin dana ciyayi da kuma takin zamani.

Bugu da ƙari yace idan yawan alúmar duniya ya ƙaru misali miliyan dubu tara ne ko goma ko kuma sha ɗaya, to zai zama wajibi a ruɓanya neman sabbin dabaru na bunƙasa noman ta hanyar zamani, saboda ƙarancin ƙasar noma, a hannu guda da matsalar Hamada da ake fama da ita.

A nasa ɓangaren Rudolf Buntzel na ƙungiyar mujamaú masu bada taimakon ayyunkan bunƙasa cigaba, yace taimakon da manyan kamfanoni kamar BASF da Bayer da DuPont, Monsato da Syngenta za su bayar domin tallafi ga Afirka ba wata gudunmawa ba ce ta azo a gani ba, idan aka kwatanta da amfanin da ƙasashen Afirkan za su samu idan aka buɗe musu hanyoyi da zasu bunƙasa cinikin kayan amfanin gonar su da ƙasashen waje. yace ko da yake yan shekaru da suka wuce an yi nasarar bunƙasa noma a Nahiyar Asia ta hanyar shirin Green revolution, amma yanayin ba ɗaya bane da Afirka.

"Yace matakin farko na shirin Green Revolution da aka yi a Asia shine an samar da irin shuka mai kyau na shinkafa da Masara da wake wanɗada masana kimiyyar aikin gona suka gudanar da bincike mai zurfi akan su suka kuma inganta su yadda za su dace da irin yanayin ƙasar, to amma lamarin ba haka yake ba a Afirka domin kusan babu cibiyoyin bincike na gwamnati kan shaánin noma, yawancin waɗanda ake da su a yau na yan kasuwa ne masu zaman kan su. A yau manyan kamfanonin noma sun cika ƙasashen Afirka da iri na kayan gona waɗanda ba na gargajiya ba".

Buntzel ya ƙara da cewa fiye da kashi 80 cikin ɗari na manoman Afirka ƙananan manoma ne, kuma sauyin dabarun shuka kamar abin da aka shuka bara ba shi zaá noma a bana ba, da inganta hanyoyin kasuwanci amfani gona a cikin gida sune ya kamata a bada himma akan su domin taimakawa manoma.

"Yace akwai misalai da aka gani kamar a ƙasar Kenya inda manoman lambu kimanin 60,000 aka haɗe su wuri guda domin basu horo da kuma shawarwari. Da farko abin gwanin shaáwa to amma a yanzu daga cikin manoman nan 60,000 manoma 15,000 ne kawai suke cigaba da noman a halin yanzu. Saboda haka wannan tsari ne irin na Bankin Duniya ko dai ka rugumi tsarin zamani ko kuma ka tattara ka san na yi".

Jamín ƙungiyar bada taimakon ta mujamár Protestant Rudolf Buntzel yace manyan kamfanonin ba wai suna taimakawa manoma ne domin Allah ba, suna yi ne domin wata manufa ta su ta daban yadda a nan gaba manoman Afirka za su rika noma irin abin da waɗannan kamfanoni suke buƙata amma abin da su manoma suke da shaáwa akan sa ba.