1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar zaman lafiyar Lebanon bayan kisan Hariri

February 15, 2005

Manazarta al'amuran yau da kullum na tababa a game da makomar zaman lafiyar kasar Lebanon bayan kisan gillar da aka yi wa tsofon P/M Rafik Hariri

https://p.dw.com/p/Bvd8

An dai sake shiga wani mawuyacin hali na yamutsi a yankin gabas ta tsakiya. Wata dake aika wa tashar telebijin ta LBC dake zaman kanta a kasar ta Lebanon, wacce ta halarci dandalin ta’asar domin ba da rahoto kai tsaye, kame baki tayi ta kasa magana, domin kuwa wannan harin da aka kai kan tsofon P/M kasar, ya haddasa rudami da rashin sanin tabbas a zukatan jama’a, bayan sararawar da kasar ta Lebanon ta samu daga yakin basasarta na tsawon shekaru da dama. An saurara daga bakin Gilber al-Ashkar, masanin al’amuran siyasa a kasar Lebanon yana mai bayanin cewar tun da yake bai taba samun kwarin guiwar cewar kura lafa kwata-kwata ba, ballantana a yi batu a game da shiga wani sabon babi na zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a kasar ta yankin gabas ta tsakiya. Shi kuwa Abdel Wahed Badrkhan, babban editan jaridar Al-Hayat ta Lebanon bayyana takaicinsa yayi a game da cewar a daidai lokacin da ake samun kyakkyawan ci gaba a kasashen Larabawa kamar Iraki da Palasdinu sai ga shi ita Lebanon tana neman sake komawa gidan jiya. Matsayin da al’umar Lebanon zasu dauka a game da makomar zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar ta su sakamakon kisan gillar da aka yi wa tsofon P/M Rafik Hariri ya danganta ne da take-taken sassan kasar ta ba sa ga maciji da juna bisa dalilai na banbancin addini da kabilanci, amma ba wani tasiri daga kasashen Isra’ila da Siriya ba. Jim kadan bayan harin da aka kai, an samu rukunoni dabam-dabam na kasar ta Lebanon dake zargin Isra’ila ko kuma Siriya da hannu dumu-dumu a wannan ta’asa. Daga cikin masu tuhumar Siriya har da Gilber al-Ashkar, wanda ya kara da bayani yana mai cewar:

Sannu a hankali an fara fuskantar alkiblar nan ta kisan kai da gangan akan duk wani dake adawa da wanzuwar sojan Siriya a kasar Lebanon. Irin wannan kisan gillar ne ya rutsa da Kamal Jumblatt. Wannan manufar a daya bangaren kuma tana mai yin nuni da tabarbarewar tsaro a kasar Lebanon ta yadda ba zata yiwu a janye sojojin Siriya da aka tsugunar da su domin kiyaye zaman lafiyar kasar ba.

Shi dai shugaban Siriya Basha al-Assad bai yi wata-wata ba wajen Allah Waddai da harin, amma abin da Gilber Ashkar ke tababa game da shi ne kasancewar a 'yan watannin baya-bayan nan kasar siriya na fama da matsin lamba daga sauran kasashe domin ta janye sojojinta dubu 25 da ta tsugunar a Arewa-Maso-Gabacin Lebanon tun bayan kawo karshen yakin basasar kasar a 1991.