1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Yawan Al'uma A Jamus

April 23, 2004

Jamus na fama da mawuyacin hali dangane da makomar yawan al'umarta sakamakon karancin haifuwa da kuma bunkasar yawan tsofaffi a kasar

https://p.dw.com/p/BvkJ
Jamus na fama da koma bayan yawan al'uma
Jamus na fama da koma bayan yawan al'uma

Cibiyar nazarin bunkasar al’uma ta Jamus dake birnin Berlin ta gudanar da bincikenta ne a kananan hukumomi da gundumomi kimanin 440 na kasar. Kuma mizanin binciken nata ya hada da yawan haifuwa ga kowane iyali da kuma yawan matasa dake kasa da shekaru 20 da haifuwa da matsayin ilimi da sana’a a dukkan yankunan. A lokacin da yake bayani a game da sakamakon da ta gano, Reiner Klingholz, darektan cibiyar cewa yayi:

Akwai babban gibi tsakanin lardunan gabaci da na yammaci da kuma arewaci da kudancin kasar. Akwai banbanc-banbance da yawa a game da ci gaban da ake samu tsakanin yankunan baki dayansu ba tare da la’akari da iyakokin jihohin tarayya ba. Manyan garuruwa da birane zasu sha fama da matsaloli kuma abin zai fi yin tsamari a gabacin Jamus.

Sakamakon binciken dai ya nuna cewar yankunan da lamarin zai fi shafa a yammacin Jamus sun hada da yankin kudu-maso-yammacin jihar Lower Saxony da arewacin jihar Hesse da kuma arewacin Bavariya. Su ma lardunan kasar da a da can suke tinkafo da ci gaban masana’antu zasu fuskanci matsala dangane da makomar yawan al’umarsu. Dangane da jihohin gabacin kasar kuwa, lamarin sai gyaran Allah saboda yankuna tara daga cikin yankuna goma sha uku da cibiyar ta gudanar da bincike kansu a can gabacin Jamus suke. Yankunan kudancin kasar da suka hada da jihar Bavariya da ta Baden-Württemberg ne kawai makomar tasu tayi gwamma. A binciken da kwararrun na cibiyar nazarin bunkasar al’uma ta Jamus dake Berlin suka gudanar dai sun gano cewar a tsakanin dukkan garuruwan Jamus, wani garin da ake kira Cloppenburg dake jihar Lower Saxony shi ne ya fi yawan haifuwa. Ta la’akari da wannan ci gaba da yawa daga cikin garuruwa da manyan biranen Jamus zasu sha fama da koma bayan yawan jama’a a cikin shekaru masu zuwa. To sai dai kuma bisa ta bakin Ines Possemeyer daga mujallar GEO dake da hannu a matakin binciken wannan ba zai yi wani tasiri na a zo a gani akan makomar yawan al’umar Jamus nan da shekara ta 2020 ba. Bisa hasashen da binciken yayi Jamus zata samu raguwar mutane kimanin dubu 660 ne nan da shekara ta 2020. Amma a daura da haka kasar zata samun baki ‚yan kaka-gida kimanin dubu 230 da zasu rika tuttudowa cikinta a duk shekara. A halin yanzu haka wadannan baki sune suka cike gibin mutane miliyan biyar da Jamus ke fama da shi idan an kwatanta da yawan jama’arta a cikin shekarun 1950. In ba tare da wadannan ‚yan kaka-gida ba yawan jama’ar kasar zai ragu zuwa mutane miliyan 51 nan da shekara ta 2050, sannan ya koma mutane miliyan 24 kacal, a shekaru 50 bayan haka. Jamus, ba shakka tana bukatar baki ‚yan kaka-gida, kuma ta la’akari da haka ya zama wajibi ta dauki nagartattun matakai na inganta sajewar wadannan baki da kuma gaurayarsu domin zaman cude-ni-in-cude-ka tare da takwarorinsu Jamusawa.